Sep 07, 2018 06:28 UTC
  • Kotun Manyan Laifuka Ta Duniya Za Ta Iya Yin Shari'ar Cutar Da Musulmin Rohigya

Kotun kasa da kasa ta manyan laifukan ce ta bayyana cewa a karkashin tsarinta da dokokinta za ta iya yin shari'a akan korar musulmin Rohingya da aka yi daga kasarsu.

A jiya alhamis ne kotun ta bayyana hakan tana kara da cewa; Ta yanke shawarar fara sauraron kara akan korar da aka yi wa musulmin Rohingya daga Myanmar zuwa kasar Bangaladesh.

A shekarar 2017 da ta gabata, fiye da musulmin Rohingya 700,000 ne su ka yi gudun hijira daga kasarsu zuwa Bangaladesh saboda kisan kare dangi da suke fuskanta daga masu tsattsauran ra'ayin addinin Bhudda.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana kisan da aka yi wa musulmin da cewa kisan kare dangi ne.

A cikin wata Agusta na wannan shekarar kwamitin da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa domin binciken abin da ya far da Musulmin Rohingya, ya bukaci kotun manyan laifuka da kasa da kasa da ta yi wa manyan jami'an sojan kasar Myanmar su biyar shari'a bisa zarginsu da hannu a kisan kare dangi.

 

Tags

Ra'ayi