Sep 07, 2018 12:12 UTC
  • UNESCO: Rabin Matasan Duniya Na Fuskantar Cin Zarafi A Makarantu

Cikin Wani Rahoto da ta fitar a Wannan alhamis, Hukumar Ilimi da Raya Al'adu ta MDD Unesco, muzgunawa da cin mutunci ya lalata karatun matasa 'yan shekaru 13 zuwa 15 kimanin miliyan 150 a Duniya

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar Sin ya nakalto Daraktan gudanarwa ta kungiyar Unesco Henrietta Fore ta ce duk da cewa ilimi shi ne tushen samarwa al'ummar kwamciyar hankali, to amma a halin yanzu makarantu sun zamantowa wasu milyoyin matasa barazana ga tsaro gami da kwanciyar hankali.

Jami'ar ta bukaci a kawo karshen wannan fargaba a makarantu, inda ta ce wasu matasan na fuskantar barazana daga abokanin karatunsu, wasu kuma daga wajen malimansu, inda rahotanin baya-bayan suka tabbatar da cin mutuncin milyoyin matasa ta hanyar yi musu fyade.

Daraktan gudanarwar na Hukumar Unesco ta kara da cewa a ko wata rana 'yan makaranta da dama na fuskantar hadari na cin mutunci, ko fadawa cikin masifin shaye-shaye, da sanun a hankali hakan ke jefa su cikin tsaro da rayuwarsu.

Tags

Ra'ayi