Sep 07, 2018 12:13 UTC
  • An Yi Yunkurin Halaka Dan Takarar Shugaban Kasa A Brazil

Wani dan takarar shugaban kasa a Kasar Brazil ya tsallake rijiya da baya a wani hari da aka kai masa yayin gangamin yakin neman zabe a arewa maso gabashin kasar

Jaridar Le Monde ta kasar Faransa ta habarta cewa wani mahari ne ya dabawa dan takarar shugaban kasar ta Brazil mai suna Jair Bolsonaro  wuka a ciki, lokacin da ya ke yi wa  magoya bayansa jawabi a birnin Juiz fora dake kudu maso yammacin kasar,  inda nan take aka ruga da shi zuwa asibiti.

Shugaba Micheal Temer ya yi allawadai da harin, yana mai cewa abu ne da ba za a amince da shi ba a kasar da take bin tsarin dimukradiyya.

Magoya bayansa sun ce an yunkurin halaka dan takararsu ne da ake ganin zai lashe zaben kasar taBrazil.

Likitoci sun ce yana cikin mummunan hali duk da ya farfado bayan nasarar tiyata cikin sa'o'I biyu da aka yi masa.

'Yan sanda sun ce sun cafke maharin nan take bayan da ya kai harin.

Tags

Ra'ayi