Sep 08, 2018 06:54 UTC
  • Trump Ya Ce Zai Sanya Karin Haraji Kan Wasu Kayakin China Da Ke Shigowa Amurka

Shugaban kasar Amurka Donal Trump a jiya Jumma'a ya bada sanarwan cewa zai kara sanya wasu kayakin da ake shigo da so kasar Amurka daga kasar China haraji.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto shugaban yana fadar haka a jiya jumma'a ya kuma kara da cewa a wannan karon yawan harajin da za'a karba zai kai dalar Amurka biliyon 267.

Kafin haka dai shugaban yan sanya haraji kan kayakin kasar china da ke shigowa kasar na dalar Amurka billiyon 200 ne. A ranar Litinin da ta gabata ce aka fara karban haraji kan mutocin da suka shia kasar Amurka daga China. Labarin ya kara da cewa a halin yanzu harajin da aka sanyawa kayakin China sun kama daga kashi 58 zuwa 172 cikin 100ne. 

A shekara ta 2017 da ta gabata harajin da ake karba kan mutocin China da suke shiga Amurka dalar Amurka miliyon 388 kadai ne.

A cikin watan Maris da ta gabata ce Amurka ta fara sanya haraji mai yawa kan kayayakin kasar Rasha wanda ya bude kofar yakin tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

Tags

Ra'ayi