Sep 09, 2018 07:32 UTC
  • An Gano Wani Shirin Amurka Na Kifar Da Gwamnatin Shugaba Maduro Na Venezuela

Jaridar New York Times ta Amurka ta ba da labarin wata ganawa ta sirri da ta gudana tsakanin wasu jami'an Amurka da wasu jami'an sojin Venezuela da nufin shirya juyin mulkin soji da kifar da gwamnatin shugaba Nicolas Maduro ta kasar.

Jaridar ta ce wasu majiyoyi sun tabbatar mata da cewa an gudanar da tarurruka daban-daban tsakanin wasu jami'an Amurka tare da wasu jami'an sojin kasar Venezuela ciki kuwa har da wani tsohon kwamandan sojin kasar wadanda suke son shirya juyin mulkin soji wa shugaba Maduron.

Tashar Talabijin din CNN ta Amurka ma ta tabbatar da wannan labarin inda ta ce wasu jami'an Amurka na yanzu da kuma na baya sun tabbatar mata da wannan labarin na gudanar da wani taro na sirri tsakanin wadannan bangarori biyu da nufin kifar da gwamnatin Maduro.

A baya ma dai shugaba Maduron ya zargin gwamnatin Trump ta Amurka ta kokarin yi masa juyin mulki da kuma kashe shi musamman bayan wani hari da aka kai masa a kwanakin baya a birnin Caracas, babban birnin kasar ta Venezuela. 

Kafafen watsa labaran Amurkan a  watan Augustan shekarar bara sun ba da rahoton cewa shugaba Trump din ya ba da umurnin zama cikin shirin kai wa kasar Venezuelan hari na soji.

 

Tags

Ra'ayi