Sep 09, 2018 19:16 UTC
  • MDD Ta Bukaci A Yi Watsi Da Hukuncin Kisa Kan Mabiya Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi

Hukumar kare hakin bil-adama ta MDD ta bukaci gwamnatin Masar da ta yi watsi da hukuncin kisa da ake yankewa fursunonin siyasa cikin harda Shugabanin kungiyar 'yan uwa musulmi.

Tashar talabijin din Aljazeera ta nakalto Michelle Bachelet babbar kwamishiniyar hukumar kare hakin bil-adama ta MDD na cewa hukuncin da kotun  hukunta manyan laifuka ta Masar ke yankewa   fursunonin siyasa na kasar bai dace ba, sannan matakin da aka bi na kame 'yan adawar  shugaba  Abdel Fattah el-Sisi a shekarar 2013 babu adalci cikinsa. 

Har ila yau hukumar kare hakin bil-adama ta MDD ta yi alawadai da yanke hukuncin kisa kan wasu 'yan 'kungiyar Ihwanul-Muslimin su 75 a kasar ta Masar, tare da bayyana hukunci a matsayin  abin kunya.

A jiya Asabar ne, Kotun da ke shari'ar manyan laifuka ta birnin Alkahira na kasar Masar ta yanke hukuncin kisa kan 'yan kungiyar Ihwanul-Muslimin su 75 tare da zartar da hukuncin daurin rai da rai a gidan kurkuku kan wasu 46 na daban.

Tags

Ra'ayi