Sep 10, 2018 05:52 UTC
  • Kerry: Ficewar Trump Daga Yarjejeniyar Shirin Iran Na Nukiliya Na Tattare Da Hadari

Tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ya sake caccakar shugaban kasar ta Amurka Donald Trump, dangane da ficewar da ya yi daga yarjejeniyar da aka cimmawa kan shirin Iran na nukiliya.

Kamfanin dillancin labaran Fars ya bayar da rahoton cewa, a zantawar da ya yi jiya Lahadi da tashar CNN, tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ya bayyana cewa, Donald Trump ya dauki salon siyasa mai matukar hadari, musamman ma ficewarsa daga yarjejeniyar shirin Iran na Nukiliya, domin hakan ya tabbatar da gaskiyar masu cewa Amurka ba abin dogaro ba ce.

John Kerry ya kara da cewa, wannan yarjejeniya an gudanar da ita ne bisa dukkanin ka'idoji na kasa da kasa, saboda ficewar Amurka daga yarjejeniyar na nufin cewa Amurka ta yi fatali da kai'doji da dokoki na kasa da kasa., ba tare da wani dalili da zai iya gamsar da duniya ba.

A ranar 8 ga watan Mayun da ya gabata ne dai Trump ya sanar da ficewar Amurka daga wannan yarjejeniya, lamarin da ya fuskanci kakkausar suka daga dukkanin bangarori na duniya.

Tags

Ra'ayi