Sep 10, 2018 18:56 UTC
  • An Bayyana Sakamakon Zaben Gama Gari Na kasar Rasha

Hukumar zabe a kasar Rasha ta bayyana sakamakon zaben gama gari wanda aka gudanar a jiya lahadi a yau litinin.

Majiyar muryar JMI daga birnin Mosco ta bayyana cewa sakamako mai jan hankali shi ne nasarar da magajin garin birnin Mosco Sergaey Sobyanin ya samu na ci gaba da kasancewa magajin garin birnin.

Amma sauran sakamakon ya nuna cewa jam'iyyar "Rasha guda" mai mulki ta fadi a yankunan  Irkutsk,  Khakassia da kuma Ulyanovsk. Sai kuma a yankunan  Khabarovsk da  Vladimir babu dantakarar da ya sami kashi akalla kashi 50% da ake bukata don samun nasara, don haka za'a je zagaye na biyu na zabe a wadannan yankuna. 

An bada sanrawan cewa kashi 30% na mutanen birnin Mosco babban birnin kasar suka fito don kada kuri'unsu. Zaben na jiya Lahadi dai an gudanar da shi don zaben magajunan gari yan majalisar dokokin yankunan da kuma cike kujeru 7 na majalisar dokokin kasar.

 

Tags

Ra'ayi