Sep 11, 2018 04:46 UTC
  • Hukumar IAEA Ta Sake Jaddada Cewa Iran Tana Ci Gaba Da Girmama Yarjejeniyar Nukiliya

Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA) ta sake jaddada cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na ci gaba da girmama yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma da ita.

Kamfanin dillancin labaran Hukumar Gidan Radio da Talabijin na Iran ya bayyana cewar hukumar ta IAEA ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwar da ta fitar a jiya Litinin a ranar farko na zaman majalisar alkalan hukumar da ke gudana a birnin Vienna, inda ta ce Iran tana ci gaba da ba ta hadin kai.

Shi ma a nasa bangaren babban daraktan hukumar Yukiyo Amano, a jawabin da yayi wajen taron, ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana ci gaba da girmamawa da kuma kiyaye dukkanin abin da aka cimma da ita cikin wannan yarjejeniyar.

A jiya Litinin din ne dai majalisar alkalai ta hukumar ta IAEA ta fara gudanar da zamanta na kwanaki biyar a birnin na Vienna da nufin tattauna hanyoyin karfafa alaka ta kasa da kasa a fagen amfani da makamashin nukiliya bugu da kari kan safarar sinadarorin nukiliya din da nufin tabbatar da tsaro da zaman lafiyan duniya.

Tags

Ra'ayi