Sep 11, 2018 12:50 UTC
  • Rundunar Sojin Rasha Ta Fara Gudanar Da Wani Atisayi Mafi Girma A Gabashin Kasar

Ma'akatar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa a yau rundunar sojin kasar ta fara gudanar da wani atisayi mafi girma a yankin gabashin kasar.

A cikin wani bayani da ta fitar a yau, Ma'akatar tsaron kasar Rasha ta bayyana cewa rundunar sojin kasar ta fara gudanar da wani gagarumin atisayi mafi girma a yankin Saberia.

A yayin wannan atisayi dai za a gwada wasu daga cikin sabbin makaman da Rasha ta kera, da suka hada makamai masu linzami da kuma tankokin yaki da jiragen yaki daban-daban.

Fiye da sojojin Rasha 300,000 ne suke gudanar da wannan atisayi, wanda yake  a mtsayin wata babbar alama ta shirin da Rasha take da shi na tunkarar duk wata barazanar tsaro daga wata kasa ta duniya.

Tags

Ra'ayi