Sep 12, 2018 11:52 UTC
  • Magoya Bayan Gwamnatin Venezuela Sun Yi Allawadai Da Shishigin Amurka A Cikin Lamuran Kasar

Dubban masu goyon bayan gwamnatin shugaban Nicolas Madoro na kasar Venezuela sun gudanar da zanga zangar yin allawadai da shishigin da gwamnatin Amurka take yi a cikin lamuran kasar.

Jaridar Heral Tribune ta yankin Laten Amurka ta bayyana cewa dubban magoya bayan gwamnatin kasar Venezuela ne suka gudanar da zanga zanga a birnin Caracas babban birnin kasar Venezuela a jiya talata inda suka yi Allawadai da kokarin juiyin mulki wa gwamnatin shugaban Nicolas madoro wanda gwamnatin kasar Venezuela ta yi. 

daga cikin wadanda suka shiga wannan zanga zangar har da Diosdado kakakin majalisar dokokin kasar ta Venezuela, wanda kuma ya fadawa jaridar Tribune kan cewa a shirye suke su kare kasarsu daga shishigin kasashen waji ko da kuwa da makami ne. 

A makon da ya gabata ne labarin ganawar jami'an gwamnatin Amurka da wasu sojojin kasar ta  Venezuela, tare da taimakon wasu kasashe makobta ya yadu. 

Tags

Ra'ayi