• John Kerry Ya Yi Gargadi Akan Siyasar Waje Ta Amurka

Tsohon ministan harkokin wajen kasar Amurkan ya fadawa jaridar Los Angeles Times cewa; Shigar da siyasa a cikin kuda da kuma wasa da harkokin zabe suna cikin muhimman matsalolin da siyasar Amurka take fuskanta a yanzu

Kerry ya kuma maimaita yin suka ga shugaban kasar Amurka musamman yadda yake mu'amala da kafafen watsa labaru da kuma hanyoyin sadarwa na al'umma.

Kerry ya bayyana shugaban kasar Amurka cewa; Donald Trump mutum ne mai rauni.

Tsohon ministan harkokin wajen kasar ta Amurka yana cikin na gaba-gaba masu sukar gwamnatin Donald trump dangane da siyasar cikin gida da kuma waje.

Ana bayyana Kerry a matsayin daya daga cikin ''yan takarar shugabancin kasar Amurka a karkashin jam'iyyar Democrat.

A cikin hirar da jaridar ta Los Angeles Times ta yi da shi, Kerry bai kore cewa zai tsaya takara ba a zaben shekarar 2020

 

Tags

Sep 17, 2018 13:09 UTC
Ra'ayi