Sep 18, 2018 14:59 UTC
  • Syria: Wani Jirgin Sojin Rasha Ya Bace A Daren Jiya A Kusa Da Birnin Latakia

Wani jirgin sojin Rasha ya bace a daren jiya, a daidai lokacin da Isra'ila take kaddamar da wasu hare-hare a birnin Latakia da ke gabar ruwa a arewa maso yammacin kasar Syria.

Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa, jirgin mallakin rundunar sojin kasar ne, kuma yana dauke da sojojin Rasha su 14 da suke hidima a sansanin sojin Rasha da ke Latakia, kuma an daina jin duriyarsa ne a lokacin da wasu jiragen yakin Isra'ila guda samfurin F-16 suke harba makamai masu linzami a kan wata cibiyar bincike da ke garin na Latakia.

Yanzu haka dai an shiga gudanar da bincike kan makomar jirgin da kuma mutanen da yake dauke da su, yayin da Amurka ta yi riga malam masallaci inda ta ce tana zaton cewa makaman kariya na rundunar sojin Syria ne suka harbo jirgin na Rasha, a lokacin da suke suke kakkabo makaman da jiragen yakin Isra'ila suke harbawa.

Ko a daren Litinin da ta gabata ma Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta harba makamai masu linzami a kan babban filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Damascus, amma makaman kariya na rundunar sojin kasar Syria sun kakkabo mafi yawan makaman.

Tags

Ra'ayi