Sep 19, 2018 05:37 UTC
  • Kotun ICC Ta Fara Gudanar Da Bincike Kan Kisan Kiyashin Da Aka Yi Wa Musulman Rohingya

Kotun duniya mai shari'ar manyan laifuffukan yaki (ICC) ta sanar da fara gudanar da bincike kan kisan kiyashi da sauran nau'oi na cin zarafin da sojojin kasar Myammar suka yi wa musulmin Rohingya na kasar.

Babbar mai shigar da kara a kotun ta ICC, Fatou Bensouda, ce ta sanar da hakan cikin wata sanarwa da ta fitar inda ta ce tuni ta fara gudanar da bincike kan dalilan da ke gaban kotun da nufin fara gudanar da cikakken bincike matukar dai dalilan da suke hannu suka tabbatar da bukatar hakan.

Bensouda ta ce binciken farko-farkon zai yi dubi cikin zargin take hakkokin bil'adama da cin zarafin da aka yi wa musulman na Rohingya da ya tilasta musu yin gudun hijira da barin matsugunansu cikin kuwa har da take musu hakkokinsu, amfani da karfi a kansu, fyade da kuma lalata musu dukiyoyinsu da dai sauransu.

Wannan sanarwa ta kotun ICC din ta zo ne a daidai lokacin da MDD take sake kira da a gurfanar da manyan jami'an sojin kasar Myammar din saboda laifin kisan kiyashin da ake zargin sun aikata a kan musulmin na Rohingya.

Dubun dubatan musulmin Rohingya din ne dai aka kashe wasu kuma aka kama da ci gaba da tsare su bayan aiwatar da nau'oi daban-daban na cin zarafi ciki har da fyade da kuma sanya wa gidajensu wuta da sojoji da 'yan daban mabiya addinin Buddha suka yi musu tsakanin watan Nuwamban 2016 da Augustan 2017.

 

Tags

Ra'ayi