Sep 23, 2018 17:42 UTC
  • Rasha: Isra'ila Ce Take Da Alhakin Harbe Jirgin Yakin Kasar Rasha

Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta gabatar da cikakken rahoto dangane da yadda aka harbo jirgin yakin kasar a lardin Lazikiyya na kasar Siriya tana mai dora alhakin faruwar hakan a wuyanharamtacciyar kasar Isra'ila.

Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rashan ya ba da rahoton cewa kakakin ma'aikatar tsaron kasar Rashan Igor Konashenkov ne ya bayyana hakan a wata ganawa da yayi da manema labarai inda ya ce "Isra'ilan' ta yaudari kasar Rashan ne ta hanyar ba ta bayanai marasa inganci dangane da wajajen da take son kai hare-hare ta sama, hakan ne ya sanya jirgin yakin Rasha ya gagara isa ga waje mai cikakken tsaro.

Har ila yau yayin da yake bayanin cewa sojojin HKI sun sanar da Rasha cewa za su kai hari a arewacin Siriya, amma sai kuma suka kai hari yammacin kasar, yana mai cewa sanarwar ma ta Isra'ila ya zo a daidai lokacin da suka fara kai harin, yana mai cewa jiragen yakin HKI sun yi amfani da jirgin yakin Rashan ne a matsayin wata garkuwa a gare su.

A ranar 17 ga watan Satumban nan ne dai sojojin Siriya suka harbo wani jirgin sojojin kasar Rasha wanda ke dauke da mutane 15 a cikinsa a daidai lokacin da sojojin na Siriya suke kokarin kakkabo wasu jiragen yakin Isra'ila da suke shirin kai hari kasar Siriyan suna masu fakewa da wannan jirgi na Rashan.

Tags

Ra'ayi