Sep 25, 2018 08:09 UTC
  • Kungiyar Anesty International Ta Bukaci China Ta Kawo Karshen Azabtar Da Musulman Kasar

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta yi kira ga gwamnatin kasar China ta kawo karshen azabtara da musulmai tsiraru a kasar.

Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto Nicholas Bequelin wakilin kungiyar ta Amnety International a gabacin Asin yana kira ga kasashen duniya su takurawa gwamnatin kasar China don kawao karshen takurawa musulmi kimani musulmai miliyon guda da suke rayuwa a lardin Kiyang dake arewa maso yammaci kasar.

Rahoton ya kara da cewa musulmi yan kabilar Uwigur a lardin Kiyong suna fuskantan dauri, azabtarwa da kuma dauri a gidajen yari daga hannun jami'an tsaron kasar ta China sanadiyyar akidarsu. 

Tags

Ra'ayi