Sep 25, 2018 17:25 UTC
  • Tattaunawa Ce Mafita Don Magance Sabani Da Iran_Macron

Shugaba Emanuelle Macron, ya bayyana cewa tattaunawa da hadin gwiwa ta kasashen duniya ce hanyar magance sabanin da ake da shi da Iran.

Mista Macron wanda ke bayyana hakan a jawabinsa a babban taron majalisar dinkin duniya, ya bayyana cewa lokacin matsin lamba da barazana ya wuce, kamata ya yi a zauna a tattauna don magance duk wani sabani da ake dashi.

Bayanan na Macron na zuwa ne bayan jawabin da Shugaban kasar Amurka ya yi inda ya nemi kasashen duniya dasu maida Iran saniyar ware.

Trump dai na zargin Iran da taimakawa ayyukan ta'addanci da kuma yi wa Amurka da Isra'ila barazana.

A farkon jawabinsa Tarum ya ce shi ne wani shugaban Amurka da ya yi abunda shugabancin Amurkar da suka gabace shi basu taba yi ba, saidai jama'ar dake babban zauren MDD, suka fashe da dariya.

Yau ne dai shugabannin kasashe dana gwamnatocin kasashen duniya suka fara jawabi a babban taron zauren Majalisar Dinkin Duniya kashi na 73 a birnin New York, in da suke gabatar da  jawabi kan halin da duniyar ke ciki.

 

 

Tags

Ra'ayi