Oct 13, 2018 11:52 UTC
  • An Kalubalanci Zaben Kasashen Bahrain Da Kamaru A kwamitin Kare Hakkin Bil Adama

Kungiyoyon kare hakkin bil adama na kasa da kasa sun kabulanci zaben kasashen Baharain, Kamaru da Philippines a kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya.

A jiya ne dai kasashe mambobin Majalisar suka zabi sabbin mambobin kwamitin inda kasashen da suka hada da Bahrain, Kamaru da Philippines suka samu wakilci a kwamitin.

Hakani zai baiwa kasashen kasancewa cikin kwamitin na tsawan shekaru uku masu zuwa daga 2019-2021.

Saidai kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasashen Turai da Amurka da kuma Canada da dama ciki har da Human Rights Watch sun kalubalnci zaben kasashen wanda suka ce bai bada misali mai kyau ba a kokarinda ake na kare hakkin bil adama, hasali ma zai kara munana batun a irin wandanan kasashen. 

Tags

Ra'ayi