Oct 19, 2018 10:18 UTC
  • Rahotanni: Maganar Sauke Muhammad bn Salman Daga Matsayin Yarima Mai Jiran Gado Na Kara Karfi

Rahotannin da suke fitowa na nuni da cewa gidan sarautar Saudiyya ya fara tunanin sauke Yarima mai jiran gado na kasar Muhammad bin Salman da maye gurbinsa da dan'uwan Khalid sakamakon irin rikicin da Bn Salman din yake janyo wa gidan sarautar da kuma ma kasar baki daya.

Jaridar Le Figaro ta kasar Faransa ta buga rahoton cewa wata majiyar diplomasiyya ta shaida mata cewa majalisar bai'ah ta kasar Saudiyyan ta gudanar da wani taro na sirri don tattauna batun bacewar dan jaridar kasar Jamal Khashoggi wanda ake ganin gwamnatin Saudiyyan ta kashe shi ne a karamin ofishin jakadancin kasar da ke Turkiyya bisa umurnin Bin Salman, inda mahalarta taron suka tattauna kan yiyuwar sauke Muhammad bn Salman daga wannan matsayi da yake kai.

Jaridar ta ce 'yan wannan majalisar wadanda su ne suka nada Muhammad bn Salman din a kan wannan matsayi a bara (2017) a halin yanzu sun fara tunanin sauke shi da kuma nada dan'uwansa Khalid bn Salman wanda shi ne jakadan Saudiyyan a Amurka sannan kuma mataimakin yarima mai jiran gadon a wannan matsayi don rage irin matsalolin da Muhammad bn Salman yake janyo wa kasar.

Tun dai bayan darewarsa karagar mulkin yarima mai jiran gadon, Muhammad bn Salman ya sanya Saudiyyan cikin matsaloli da suka hada yakin kasar Yemen, lalata alaka da Qatar yanzu kuma ga batun kisan gillan da aka yi wa Khashoggin.

 

Tags

Ra'ayi