Oct 21, 2018 18:59 UTC
  • Rasha Ta Gargadi Amurka Kan Ficewa Daga Yarjejeniyar Makamai

Rasha ta yi gargadin cewa matakin da Donald Trump ya dauka na fitar da Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar da ke tsakaninsu bahaguwar dubara da bazata kai kasar ga ci ba.

Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Sergei Ryabkob ya ce ficewar Amurka daga yarjejeniyar  kayyade adadin makamain nukiliyar da kowacce kasa za ta rika kerawa a kowacce shekara na a matsayin mafi munin ficewa daga yarjejeniya da Trump zai yi , idan aka yi la’akari da yadda kai tsaye za ta iya shafar hatta da tsaron daidaikun kasashe.

Har ila yau mataimakin Ministan ya ce, ficewar Amurka daga yarjejeniyar zai haddasa yaduwar muggan makamai a sassan duniya wanda kuma ke barazana ga tsaron al’umma.

A jiya asabar ne dai Shugaban kasar Donald Trump ya sanar da aniyarsa ta fita  daga yarjejeniyar  kayyade adadin makaman da manyan kasashen ke kerawa.

Sergei Ryabkob ya yi ikirarin cewa matukar Amurkan ta dage kan aniyarta, ba shakka babu  zabin da ya ragewa Rasha face suma su dauki matakan ramuwar gayya ciki kuwa harda fasahar soji.

Tun a shekarar 1987 shugaba Ronald Reagan ya sanya hannu kan yarjejeniyar wadda ke da nufin kayyade yawan makaman da kowacce kasa za ta rika kerawa kowacce shekara.

Ra'ayi