Nov 11, 2018 17:14 UTC
  • Dakarun Yemen Sun Sake Dakile Kokarin 'Yan Mamayan Saudiyya Na Kame Hudaydah

Jami'an kasar Yemen sun bayyana cewar dakarun kasar sun sami nasarar dakile wani kokari na kasar Saudiyya na kame garin Hudaydah da ke bakin ruwar kasar inda suka kashe da kuma kame wani adadi na sojojin haya 'yan kasar Sudan.

Rahotanni sun bayyana cewar a yau Lahadi an yi gagarumin gumurzu tsakanin sojojin sa kai na Saudiyya din da dakarun kasar Yemen da na sa kai 'yan kungiyar Al-Houthi a kokarin da Saudiyyan take yi na kame garin bakin ruwan na Hudaydah, inda suka fuskanci gagarumar turjiyya daga wajen dakarun kasar Yemen din.

Tun kimanin kwanaki goman da suka gabata ne dai Saudiyya da kawayen nata suke kokarin kutsawa da kuma kame tashar bakin ruwan na Hudaydah wanda nan ne babbar tashar da ake kai kayayyakin agaji kasar ta Yemen, sai dai har ya zuwa yanzu sun gagara kame wajen.

Wasu majiyoyi sun ce kimanin sojoji 60 ne suka rasa rayukansu daga bangarori biyun.

Har ila yau wasu majiyoyin sun ce mafi yawa daga cikin sojojin mamayan da aka kashe sojojin sa kai ne na kasar Sudan da aka shigo da su don ba da dauki ga sojojin Saudiyyan da kawayenta da suke son mamaye kasar.

 

Tags

Ra'ayi