Nov 15, 2018 05:53 UTC
  • Karfin Sojin Amurka Ya Ragu Gaban China Da Rasha

Wani rahoto da majalisar dokokin Amurka ta fitar ya nuna cewa kasar zata iya kwasar kashinta a hannu mudin ta shiga yaki da kasashen China ko Rasha.

Rahoton wanda kwamitin majalisar kan dabarun tsaron kasar ya fitar a jiya Laraba, ya ce kasar na fuskantar babban kalubale a bangaren soji, kuma zata iya shan kashi ko kuma ta sha wahala sosai a duk wani yaki da zata shiga da Rasha ko China, wanda hakan zai janyo mata hasara rayukan sojoji fiye da yadda ake tsammani.

Kwamitin 'yan majalisun da ya kunshi mambobi 12 tsofafin manyan jami'an kasar daga bangaren jam'iyyun siyasa na Democrat da na Repablican, ya ce duk da ma'aikatar tsaron Amurka na ware kasafin kudi da ya kai Dala Biliyan 700, sama da kudaden da kasashen China da Rasha su biyu ke kashewa kan sha'anin tsaronsu, kasafin kudin da gwamnatin Trump ke ware wa don cimma burinta kan dabarun tsaron kasar ya yi kadan.

A don haka kwamitin ya fitar da shawarwari da dama ciki har da bukatar karin kashi 3 zuwa 5 akan kasafin kudin da ake ware wa sha'anin tsaron kasar. 

Ra'ayi