Nov 16, 2018 06:38 UTC
  • Kungiyar Kare Hakkin Bil'adama ta

A jiya alhamis ne kungiyar kare hakkin bil'adaman ta kasa da kasa ta fitar da wani bayani da a ciki ya bayyana cewa binciken da Saudiyya ta ce ta gudanar ba abin dogaro ba ne.

Bayanin na kungiyar kare hakkin bil'adaman na kasa da kasa ya ci gaba da cewa; Da akwai bukatar Majalisar Dinkin Duniya ta gudana da bincike nata mai zaman ganshi akan kisan dan jaridar na kasar Saudiyya Jamal Kashogi, domin gano hakikanin abin da ya faru.

A ranar 2 ga watan Oktoba ne dai Jamal Kashoogi ya bace bayan shigarsa cikin karamin ofishin jakadancin kasarsa Saudiyya da yake a birnin Istanbul na kasar Turkiya.

Sai bayan kwanai 18 daga bacewar dan jardiar mahukunatan Saudiyya suka sanar da cewa ya mutu, bayan fada da ya faru a tsakaninsa da masu bincike a cikin karamin ofishin jakadancin

Sai dai kasashen duniya da dama ba su aminta da riwayar ta mahukuntan Saudiyyar ba tare da fara yin kiraye-kiraye da a yi wani binciken na kasa da kasa mai zaman kanshi

Ra'ayi