Nov 19, 2018 05:10 UTC
  • Dakarun Yemen Sun Amince Da Kiran MDD Na Dakatar Da Kai Hari Kan Saudiyya Da Kawayenta

Dakarun Ansarullah na kasar Yemen, wadanda suke ci gaba da kare kasar daga hare-haren wuce gona da irin Saudiyya da kawayenta sun amince da kiran da MDD ta yi musu na su dakatar da kai hare-hare kan Saudiyya da kawayen nata don share fagen ci gaba da tattaunawar tsagaita wuta a kasar.

Dakarun na Ansarullah wadanda aka fi sani da 'yan Houthi sun sanar da hakan ne cikin wata sanar da suka fitar a yau din nan Litinin inda suka ce sun amince da batun tsagaita wuta ne din ne wanda manzon musamman na MDD Martin Griffiths ya gabatar musu.

Har ila yau kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo shugaban kwamitin koli na juyin juya halin kasar Yemen din Mohammed Ali Al-Houthi yana fadin cewa bayan dakarun Houthi din sun sanar da wannan matsaya ce bayan tattaunawar da suka yi da manzon MDD wanda ya bukace su da su dakatar da kai hare-hare da makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan masu wuce gona da irin.

Sanarwar dakatun Ansarullah din ta zo ne bayan Saudiyya da kawayen nata sun sanar da dakatar da hare-haren da suke kai wa tashar bakin ruwan nan na Hudaidah wanda suke son kwacewa don hana shigo da kayan agaji ga al'ummar ta Yemen.

 

Tags

Ra'ayi