Nov 20, 2018 09:27 UTC
  • Kokarin Iran Da Turai Akan Kasar Yemen Ya Haifar Da Sakamako Mai Kyau

Babbar jami'a mai kula da siyasar waje da kuma tsaro ta tarayyar Turai, Friedrica Mugrini ce ta bayyana hakan dangake da kokarin kawo karshen yakin kasar Yemen

Jami'ar ta harkokin wajen turai ta kuma ce; Tattaunawar da aka yi ta tsawon watanni ta haidar da sakamako mai kyau.

Jamhuriyar musulunci ta iran wacce take a matsayin daya daga kasashe masu tasiri a yankin gabas ta tsakiya, tana kokarin ganin an sami zaman lafiya mai dorewa a cikin yankin

Saudiyya ta shelanta yaki akan kasar Yemen tun daga shekarar 2015 wanda yawo ya zuwa yanzu ya ci rayukan fiye da mutane 13,000 yayin da wasu dubun dubatar kuma su ka jikkata. Bugu da kari hare-haren da Saudiyyar ke kai wa kasar ta Yemen sun lalata asibitoci da kuma cibiyoyin shan magani a fadin kasar

A halin da ake ciki a yanzu kasar ta Yemen tana fuskantar karancin abinci da kuma magani

Tags

Ra'ayi