Nov 26, 2018 17:26 UTC
  • Kungiyoyin Kare Hakkokin Bil'adama Na Tunusiya Za Su Gudanar Da Zanga-Zangar Kin Jinin Ziyarar Bin Salman

Kungiyoyin kare hakkokin bil'adama daban-daban na kasar Tunusiya sun sanar da cewa za su gudanar da wani gagarumin gangami don nuna rashin amincewarsu da ziyarar da Yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya, Yarima Muhammad Bin Salman zai kawo kasar don nuna rashin amincewarsu da kisan gillan da Saudiyya ta yi wa dan jarida dan kasar Jamal Khashoggi.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo Soukaina Abdessamad ta kungiyar 'yan jarida ta kasar Tunusiyan tana sanar da hakan inda ta ce al'ummar kasar Tunisiya ba sa maraba da zuwansa (Bin Salman) don kuwa yana kokarin amfani da ziyarar ce wajen wanke kansa daga kisan gillan Khashoggi. Don haka ta ce za su gudanar da zanga-zanga tun daga yau Litinin har zuwa gobe Talata.

Sanarwar dai ta ce kimanin kungiyoyin kare hakkokin bil'adama 13 cikin kuwa har da kungiyar 'yan jaridu ta kasar Tunusiyan suna sanar da shiga cikin zanga-zangar da za a gudanar don nuna kiyayya da ziyarar Bin Salman din.

A gobe Talata ce dai ake sa  ran Yarima Muhammad bin Salman din zai kai ziyarar aiki kasar Tunusiyan a ci gaba da ziyarar da ya shirya kai wa wasu kasashen Larabawa a abin da wasu suke ganin kokari ne da gwamnatin Saudiyyan take yi na nuna cewa Yarima yana nan daram biga karagar mulkin nasa duk kuwa da ci gaba da Allah wadai da Saudiyyan da ma shi kan Bin Salman din saboda hannun da yake da shi wajen kisan gillan da aka yi wa Jamal Khashoggin.

 

Tags

Ra'ayi