Dec 08, 2018 04:16 UTC
  • Kungiyar OPEC Ta Amince Ta Rage Yawan Man Fetur Da Membobinta Suke Fitar

Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur (OPEC) da kuma wasu kasashe 10 su ma masu arzikin man fetur din da suka da kasar Rasha, sun amince da batun rage yawan man da ake samarwa a kasuwar duniya zuwa ganga miliyan daya da dubu dari biyu a rana.

Rahotanni dai sun bayyana cewar an cimma wannan matsayar ce bayan tattaunawa ta kwanaki biyu da kungiyoyin biyu suka gudanar a birnin Vienna na kasar Austria inda suka matsayar rage yawan mai din da suke fitarwa din daga ranar 1 ga watan Janairu mai kamawa na 2019 a kokarin da suke yi na kara daga farashin mai din sabanin abin da gwamnatin Amurka take so na kara rage farashin man.

Ministan man fetur din kasar Iraki Thamer Abbas al-Ghadhban ne ya sanar wa manema labarai wannan mataki da kasashen suka dauka inda ya ce daga cikin ganga miliyan 1.2 din da za a rage din kasashen kungiyar ta OPEC su 14 za su rage ganga 800,000 na man da suke fitarwa a kowace rana alhaki sauran kasashen da ba na OPEC din ba kuma za su rage ganga 400,000 na man da suke fitarwa a kowace rana.

Yarjejeniyar da aka cimma a jiya din dai ta cire kasashen Iran, Venezuela da kuma Libiya daga cikin kasashen da za su rage man fetur din da suke fitarwa lamarin da Iran din ta yi maraba da shi, don kuwa tun farko ministan man fetur na kasar Bijan Zangeneh ya bayyana cewar Iran ba za  ta amince ta rage yawan man fetur din da take fitarwa a irin wannan yanayi da take ciki da Amurka ta sanya mata takunkumi na zalunci.

 

Tags

Ra'ayi