Dec 08, 2018 04:17 UTC
  • Imran Khan: Pakistan Ba Za Ta Sake Zama 'Sojar Hayar' Amurka Ba

Firayi ministan kasar Pakistan Imran Khan ya bayyana rashin jin dadinsa da yadda alakar kasarsa da Amurka ta kasance a baya yana mai cewa a halin yanzu dai Pakistan ba za ta sake zama wata sojar hayar Amurka ba.

Firayi ministan na Pakistan ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da jaridar Washington Post ta Amurka inda yace shi dai ba zai kulla alakar da Pakistan za ta zama tamkar wata 'sojar haya' ga Amurka ba inda za a bata kudi tana yi wa wani mutum na daban yaki ba. Yana mai cewa bai kamata mu sake sa kanmu cikin irin wannan yanayin a nan gaba ba.

Yayin da yake mayar da martani da tuhumar da gwamnatin Amurka take yi na cewa Pakistan din tana ba da kariya ga 'yan ta'adda a cikin kasar, firayi minista Khan ya ce Pakistan ta yi hidima wa Amurka ne cikin yakin da tace tana yi da  ta'addanci alhali lamarin bai shafi Pakistan ba, yana mai cewa idan da a ce Pakistan din ba ta shiga cikin wannan ba, da ba ta fuskanci irin matsaloli da ta shiga ciki ba na hare-haren ta'addanci da ta dinga fuskanta ba.

Kalaman na Imran Khan suna zuwa ne bayan wasu zafafan kalamai da yayi kan shugaban kasar  Amurka Donald Trump a watan da ya wuce yana mai watsi da kalaman shugaban Amurkan na cewa  Pakistan ba ta yi komai ba a fada da ta'addanci duk kuwa da biliyoyin dalolin da ta karba  daga wajen Amurka.

 

Tags

Ra'ayi