Dec 13, 2018 19:02 UTC
  • An Kama Mutane 7 A Rasha Bisa Zargin Tallafawa Yan Ta'adda A Siriya

Hukumar tsaron cikin gida ta kasar Rasha FSB ta bada sanarwan tsare mutane 7 wadanda take tuhuma da aikawa yan ta'adda da ke kasar Siriya kudade daga kasar

Tashar talabijin ta Rasha-Today ta nakalto hukumar ta FSB tana fadar haka, ta kuma kara da cewa mutanen sun kafa wata cibiya bada agaji a shekara ta 2016 inda suke tara kudade daga wajen mutane don tallafawa yan ta'adda ta suke kasar Siriya.

Labaran ya kara da cewa mutane sun fito ne daga lardunan Mosco, Chechen, Dagistan, da kuma Ingushetia. Kuma sun fara amfani da katin banki don aika kudaden ne tun shekara ta 2010.

Gwamnatin kasar Rasha dai ta samar da shirye-shirye na musamman da dama don yaki da ayyukan ta'addanci a kasar tun bayan shigarta cikin aikin yaki da yan ta'adda a kasar Siriya.

Tags

Ra'ayi