Dec 15, 2018 19:25 UTC
  • Ana Ci Gaba Da Zanga-Zangar Nuna Kin Jinin Gwamnati A Kasar Faransa

Jaridar Lo Figaro ta kasar Faransa ta ce daruruwan masu adawa ta siyasar tattalin arziki ta gwamnati da ake yi wa kirari da masu rawayar taguwa, sun fito kan titunan birnin Paris

Ya zuwa yanzu jami'an 'yan sanda sun yi awon gaba da mutane 25 daga cikin masu Zanga-zanga yayin da aka wuce gidan kurkuku da wasu takwas

Bugu da kari a yau Asabar dubban 'yan sanda ne su ka bazu akan titunan birnin Paris da sauran biranen kasar  domin murkushe masu Zanga-zangar

Zanga-zangar ta yau, ta biyo bayan jawabin da shugaban kasar Emmanuel Macron ya yi ne da a ciki ya ja da daya akan matakai da yawa da gwamnatinsa ta dauka

Zanga-zangar dai ta fara ne akan nuna kin amincewa da karin kudaden makamashin, sai dai daga baya ta ci gaba da nuna adawa akan siyasar tattalin arziki ta jari-hujja irin wanda shugaba Macron yake aiki da shi.

 

Ra'ayi