Jan 20, 2019 19:11 UTC
  • Yawan Mutanen Da Suka Rasa Rayuansu Sanadiyar Gobara A Mexico Ya Kai 79

Yawan mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar facewa da kuma kama wutan da wani bututun mai yayi a kasar Mexico ya karu zuwa mutane 79.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalto ministan kiwon lafiya na kasar ta Mexico yana fadar haka a yau Lahadi. Ya kuma kara da cewa har yanzun halin da wasu daga cikin wadanda gobarar ta rutsa da su bai da kyau.

Umar Fayyad gwamnan jihar Hidalgo inda hatsarin ya auku ya fada cewa mutane 66 suka mutu sanadiyar facewar bututun man da kuma gobarar da ta biyo baya a jiya Asabar, kusa da wata matatan man fetur a jihar. 

Shugaban kasar ta Mexico Andrés Manuel López Obrador yayi kira ga dukkan ma'aikatun gwamnatin kasar su kai dauki gwargwadon iyawarsu ga wadannan wannan hatsarin ya shaf.

Majioyin jami'an tsaron sun bayyana cewa barayin man fetur ne suka huda bututun man don satarsa, sai gobara ta tashi a wurin. 

Gwamnatin kasar ta Mexico ta bayyana cewa ta yi asarar dalar Amurla billiyon 3 a shekarar da ta gabata sanadiyyar fasa bututun mai da kuma satar man a kasar.

Ra'ayi