Jan 23, 2019 10:38 UTC
  • An Bude Taron Tattalin Arzikin Duniya A Davos

An bude taron tattaunawar tattalin arzikin kasa da kasa na shekarar 2019 a birnin Davos na kasar Switzerland, inda mahalarta taron zasu kwashe kwanaki suna tattauna yadda za a aiwatar da shirin kyautata rayuwar al'umma.

Saidai taron na bana bai samu halartar wasu shuwagabannin manyan kasashen duniya ba, da suka hada dana Amurka, Faransa da kuma Biritaniya ba.

Shugaban Amurka Donald Trump, ya kaurace wa taron sakamakon rikicinsa da bangaren majalisa, yayin da takwanransa na Faransa Emmanuel Macron ya kaurace wa taron sakamakon matsaloli masu nasaba da tattalin arziki a cikin gida, sai kuma Fira ministar Burtaniya Theresa May wacce bata halarci taron ba, saboda takadamar dake tsakaninta da wasu 'yan siyasar kasar kan yarjejeniyar ficewar daga cikin tarayya Turai.

Kafin bude taron, asusun ba da lamuni na IMF ya gabatar da sabon bayani game da "rahoton hasashen tattalin arzikin duniya" a birnin Davos, inda ya sake rage hasashen da aka yi kan karuwar tattalin arzikin duniya na shekarar 2019 da na shekarar 2020 zuwa 3.5% da 3.6%.

Taron wanda aka fara a jiya, na samun halaratar wakilai kimanin 3000 daga gwamnatocin kasashen duniya, kungiyoyin kasa da kasa, bangaren kasuwanci da masana da dai sauransu, za su tattauna kan yadda za a bullo da sabon salon neman dauwamammen ci gaba bisa taken taron, "Dunkulewar duniya a matsayi na hudu'' a yadda za'a aiwatar da shirin kyautata rayuwar al'umma.

Ra'ayi