Feb 17, 2019 06:44 UTC
  • An Yi Ganawa A Tsakanin Ministan Harkokin Wajen Venezuela Da Manzon Musamman Na Amurka

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato ministan harkokin wajen kasar Venezuela Jorge Arreaza yana ba da labarin ganawar sirri a tsakaninsa da dan sakon musamman na Amurka Elliott Abrams

Ministan harkokin wajen kasar ta Venezuela ya kara da cewa; Gwmanatin kasar Amurka ta ayyana Elliott ne a matsayin manzon musamman zuwa Venezuela domin ganawar sirri da gwamnatin Maduro.

Sai dai minista Arreaza bai bayyana abin da tattaunawar ta kunsa ba

Gwamnatin kasar shugaba Nocolas Maduro tana zargin Amurka da kokarin yin juyin mulki, abin da ya jaza ta yanke huldar diplomasiyya da ita a ranar 23 ga watan Janairu

Shugaban majalisar dokokin kasar ta Venezuela Juan Guaidó ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa, tare da samun goyon baya daga Amurka da kasashen turai.

Sai dai kasashen Iran, Rasha, Sin sun nuna cikakken goyon bayansu ga gwamantin shugaba Nicolas Maduro.

Tags

Ra'ayi