Feb 22, 2019 04:33 UTC
  • Amurka Zata Bar Sojoji 200 A Siriya

Amurka ta sanar da cewa sojojinta kimanin 200 ne zasu ci gaba da zama a Siriya, makwanni kadan bayan da shugaban kasar Donald Trump, ya sanar da shirin janye sojojin kasar daga kasar ta Siriya.

Kakakin gwamnatin ta Amurka, Sarah Sanders, ta shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP, cewa, za'a bar kadan daga cikin sojojin na Amurka kimanin 200 don tabbtar da zaman lafiya na wani dan lokaci a Siriya.

Bayanai sun nuna cewa wannan matakin na zuwa bayan wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shugaba Trump da takwaransa na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan. 

A cikin makwanni masu zuwa ne ake sa ran Amurka zata fara kwashe sojojin nata daga Siriya, a daidai lokacin da ake tsammanin cewa an kusa murkushe kungiyar (IS) a sansaninat na karshe a Siriyar.

A ranar 20 ga watan Disamba na shekara data gabata ne shugaba Trump na AMurka ya furta cewa, '' lokaci ya yi da sojojinmu ya kamata su dawo gida, tunda mun yi nasara kan kan kungiyar ta (IS).

Matakin da kawayen na Amurka musamman na Turai, suka soka, kasancewar a cewarsu ba'a shawarce su ba, tare da kuma da ganin hakan zai kara karfafa karfin Rasha da Iran a yankin.

Tags

Ra'ayi