Mar 19, 2019 06:21 UTC
  • Dangin Mutumin Da Ya Kashe Musulmi A New Zealand Sun Nemi Gafara

Dangin mutumin da ya kashe musulmi a kasae New Zealand sun nemi gafarar musulmi da kuma sauran al’ummar kasar, dangane da abin da Brenton Tarrant ya aikata.

Kamfanin dillancin labaran Saumaria News ya bayar da rahoton cewa, kakar Brenton Tarrant a lokacin da take zantawa da wasu kafofin yada labarai ta sheda cewa, abin da ya faru shi ne abu mafi muni a tarihin iyalansu baki daya, kuma suna cikin bakin ciki maras misiltuwa dangane dangane da abin da jikanta ya aikata.

Marry Grald ta bayyana cewa, suna neman gafara daga dukkanin wadanda abin ya shafa, musamman wadanda suka rasa daninsu, da kuma wadanda suka samu raunuka sakamakon harin da jikanta ya kai a kan wurin ibadar musulmi a kasar New Zealand.

Ta ci gaba da cewa, jikan nata ya canja baki daya tun daga lokacin da ya fara yin tafiye-tafiye zuwa kasashen ketare, inda suke ganin alamun kekesar zuciya tare da shi, da rashin sauraren shawarar kowa a  cikin lamarinsa.

 

 

 

 

Ra'ayi