• An Gudanar Da Zaman Tattaunawa Tsakanin Malaman Sunna Da Shi'a

An guadanar da zaman tattaunawa a tsakanin malaman Shi'a da na sunna a kasar Pakistan, da nufin kara kusanto da fahimtar juna da kuma karfafa hadin kai a tsakanin al'ummar musulmi.

Rahotanni daga kasar ta Pakistan sun ce an gudanar da wanann zama ne a cikin gundumar Baluchestan, tare da halartar wasu daga cikin fitattun malamai na bangarorin sunna da shi'a na yankin da ma wasu yankuna na kasar ta Pakistan, da nufin karfafa fahimtar juna da kuma yaki da mummunar akidar nan ta kafirta musulmi, wadda ita ce tushen ta'addanci a halin yanzu a cikin kasashen musulmi.

Daga cikin malaman da suka halarci taron akwai Maulana Shirani, shugaban majalisar malaman sunnah a yankin Baluchestan, da kuma Sayyid Hashim Musawi, daya daga cikin manyan malaman shi'a na kasar Pakistan, kuma limamin birnin Birnin Kuita na mabiya mazhabar shi'a, gami da wakilan sauran kungiyoyin 'yan sunnah na kasar, da suka hada da 'yan salafiyyah, Jama'at Ahlu Hadis da sauransu.

Dukkanin wadanda suka halarci taron sun nuna farin cikinsu dangane da yadda taron ya gudana a cikin yanayi na 'yan uwantaka ta muslunci da girmama juna, kamar yadda kuma mahalrta taron suka bukaci da a sake farfado da kungiyar hadin kan musulmi ta kasar Pakistan wato Millat Islamiyyah Mahaz, wadda ta hada wakilan dukkanin bangarorin musulmin kasar, da suka hada da 'yan sunnah, da shi'a da kuma darikun sufaye.

Bayan kammala taron a yammacin jiya, Maulana Shirani ya jagoranci sallar Magariba wadda ta hada dukkanin bangarorin kungiyoyin musulmi da suka halarci taron.

Aug 03, 2016 18:04 UTC
Ra'ayi