Feb 22, 2016 17:13 UTC
  • Matsayin Shawara A Musulunci:

Dangane Da Zaben Majalisar Shawarar Musulunci A Iran

Zaben Majalisar Shawarar Musulunci A Iran

3

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wanann fitowar ta shirin mu leka mu gani. Shiri ne dai wanda mu ka saba gabatar mu ku da batutuwan da su ka shafi fuskoki daban-daban na rayuwa.

To har yanzu dai muna a tare da ku ne a cikin tattaunawar da mu ka bude dangane da zabukan 'yan majlisar shawarar musulunci ta Iran da kuma na majalisar kwarararru masu zaben jagoran juyin juya halin musulunci a Iran.

Da fatan za a kasance a tare da mu domin a ji yadda shirn zai gudana.

*****

Ranar juma'a wacce ta yi daidai da 26 ga watan Febrairu na wannan shekara ta 2016 ce al'ummar Iran za su fito kwansu da kwarkwatarsu domin kada kuri'a a zaben majalisar shawarar musulunci karo na goma daga tarihin juyin juya halin musulunci na Iran. Za su kuma zabi majalisar kwararru mai zabar jagoran juyin juya halin musulunci karo na biyar. Wani abu mai jan hankali anan shi ne cewa Iran ce kan gaba wajen fitowar mutane masu kada kuri'a a duk lokacin da zabe ya zo. A cikin bangare na shida na tsarin mulkin jamhuriyar musulunci ta Iran an ambaci cewa; Sha'anin tafiyar da kasa, wajibi ne ya dogara da ra'ayin mutane t ahanyar zabar shugaban kasa da wakilan majalisar shawarar musulunci da sauran majalisa da makamantansu.

A bisa tsarin mulkin na jamhuriyar musulunci ta Iran, zangon da shugaban kasa da kuma 'yan majalisa su ke yi, shekaru hudu ne kacal, kuma za a gudanar da kowane zabe ne gabanin karewar zangon wadanda su ke kan mulki, saboda ya zamana babu wani lokaci da ba a sauraron ra'ayin al'umma.

A tsakanin cibiyoyin da mutane ne su ke zabarsu, da akwai guda biyu da su ke da muhimmanci na musamman. Wadanann kuwa su ne majalisar shawarar musulunci da kuma majalisar kwararru mai zabar jagoran juyin juya halin musulunci.

Majalisar shawarar musulunci wacce ta ke da wakilai 290, tana da muhimmanci da kuma nauyi mai girma da ya rataya a wuyanta.

Ita ma majalisar kwararru wacce aikinta shi ne zabar jagoran juyin juya halil mutane ne su ke zabar mambobinta kai tsaye. Tana kunshe ne da malaman addini masana fiqhu da musulunci da kuma ma'abota tunani. Aikinsu shi ne zabar jagoran juyin juya halin musulunci.

A bisa yadda ya zo a kundin tsarin mulkin jamhuriyar musulunci ta Iran shi ne cewa; A lokacin gaiba ko fakuwar imami na 12 wato Imam Mahadi (A.J) tafiyar da sha'anin shugabanci a jamhuriyar musulunci ta Iran zai kasance a hannun jagora masanin fikhu, adali, sananan kuma ma'abocin takawa, wanda ya san zamaninsa, mai jarunta da iya tafiyar da sha'anin mulki. kuma majalisar kwararru ce za ta zabe shi.

Saboda zabar jagoran juyin abu ne mai muhimmanci, wadanda za su zabe shi, dole ne su zama kwararru da za su iya tantance wanda ya cika wadancan sharuddan da dacewa. Su kuwa za su kasance masu wakiltar al'umma ne wacce ta zabe su.

Shakka babu daya daga cikin ni'imomi mafi girma da Allah madaukakin sarkin ya yi bil'adama ita ce, nimi'ar hankali da ya ba shi.. Domin ta hanyar amfani da wannan hankalin ta hanyar da ta dace, mutum zai iya samarwa kansa da sa'ada. Da hankaline mutum zai iya zabarwa kansa hanya mafi dacewa. Daya daga cikin abubuwan da su ke tabbatar da gaskiyar aiki da hankali ita ce yadda addinin musulunci ya bada shawarar aiki da hankali ta yin shawara.

Ubangiji madaukakin sarki a cikin suratu Bakara aya ta 233 da kuma ali-Imrana aya ta 159 da kuma suratu shura aya ta 38, ya bayyana muhimmancin yin shawara a tsakanin mutane. Kuma daya daga surorin alkur'ai mai tsarki ma an ba ta sunan shura ne, wato shawara.

A addinin musulunci da akwai nau'oi na shawara da su ka zo a cikin alkur'ani mai girma. A cikin suratu ali-Imrana aya ta 159 Allah madaukakin sarki yana magana da manzon Allah (s.a.w.a):

" Ka yi shawara da su a cikin al'amari. Idan kuma ka dauki azama, ka dogara ga Allah, domin Allah yana son masu tawakakli"

Manzon Allah (s.a.w.a) yana yin biyayya ne ga wahayin da ya sauka a gare shi daga Allah madaukakin sarki, sai dai a lokaci guda yana yin shawara da musulmi wajen zartar da dokoki. Manzon Allah wanda ya ke a matsayin jagora da Alla ya aiko shi ya ba shi umarnin yin shawara kuma tarihinsa ya tabbatar da cewa haka rayuwarsa ta kasance.

A cikin hadisai da kuma riwayoyi na mazon Allah da imamai (a.s) an jaddada muhimmanci yin shawara da musayar ra'ayi da mutane. Saboda haka tabbas daukar matakai na kwarai suna a tattare da yin shawara.

Duk wata al'umma wacce bata da al'adar yin shawara to za ta rika kai kawo a cikinta, amma wacce ta ke da al'adar yin shawara za ta kasance akan tafarki mafi dacewa. Kuma kofofi za su bude wa wannan al'ummar fiye da wacce ba ta shawara.

Manzon Allah (s..a.w.a) yana fadin cewa:

"Babu wata al'umma wacce za ta yi shawar zai ta sami shirya zuwa tafarki mafi dacewa."

Bisa ka'ida, alummar da ta ke yin shawara a tsakaninta da wuya ta fada cikin matsalolin da zai sa ta ji kunya, idan aka kwatanta da wacce tsarinta na kama-karya ne. Kama karya tana tattare da fadawa cikin matsaloli da kura-kurai wajen daukar matakai da yanke hukunci.

Allamah TAba-Tabei, a cikin tafsirinsa na alkur'ani ya yi bayani a karkashin suratu Shura', ayar da ke cewa: "Al'amarinsu shawara ce a tsakaninsu."

Wadannan su ne muminai wadana su ke da girman tunani. Suna tantancewa wajen tsamo wani ra'ayi da mahanga wacce ta dace da kuma dogaro da ma'abota tunanin. Kuma ta fuskar ma'ana wannan ayar tana da kusanci wajen ma'ana da aya ta 18 a cikin suratu Zumar da ta ke cewa:

"Ka yi wa bayina bushara, wadanda su ke sauraron zance, sanann su bi mafi kyawunsa."

Tags

Ra'ayi