• Shekaru 37 Daga Cin Nasarar Juyin Musulunci

Jin Cewa Za mu iyaDaga lokacin da juyin musulunci a Iran ya kai ga samun nasara, salon  kalubalantar manyan kasashe masu takama da karfi ya sauya. Sannu a hankali wannan yunkurin ya sauya zuwa farkawar musulunci wanda ya zo a matsayin wani gagarumin ci gaba a cikin kasashen musulmi, musamman ma dai a tsakanin wadanda ake zalunta. Yankin yammacin Asiya na daga cikin wuraren da cin nasarar juyin musulunci ta yi tasiri maif girma a cikinsu.


 cin nasarar juyin musulunci a Iran ya kawo sauyi a cikin fagen siyasar kasa da kasa da kuma ta yankin gabas ta tsakiya. Ya baiwa al'ummun da ake zalunta jin cewa lallai za su iya yunkurawa.


Tun farkon juyin, manufofinsa su ka fito fili ta yadda al'ummu da dama da su ke rayuwa a karkashin zaluncin masu takama da karfi su ka fahimce su. Don haka ba abu ne mai wuya ba fahimtar hakikanin inda ya dosa.


 Juyin musulunci na Iran ta zo a matsayin wata dama ga al'ummar musulmi domin su koma ga tarihinsu na hakika. Shi ne kuma wanda ya zama mabudin bayyanar farkawar musulunci.


 Wani abu mai muhimmanci wanda juyin musulunci a Iran ya jingina da shi, shi ne

kusancin da al'ummar Iran ta ke da shi ta fuskokin al'adu. Wannan ya zama riba a cikin fagagen siyasa da zamantakewa wanda ya kai ga nuna karfin da addinin musulunci ya ke da shi.


 Wasu daga cikin abubuwan da su ka zama kirkirar juyin musulunci na Iran sun kunshi cusawa kai jin cewa za a iya cimma abinda aka sanya a gaba, da nesantar  alakanta kai ta fuskar al'adu da siyasa da yammacin turai.

Manazarta da dama sun amince da cewa juyin musulunci na Iran ya taka rawa mai girma wajen wayar da kan al'ummun da ake zalunta da raunana a cikin kasashen musulmi. Ya kuma samar da jarunta da tsayuwar daka wajen fuskantar masu zaluntarsu. Hakan kuwa ya zama wani sako ne na hadin kai a tsakanin al'ummar wajen fuskantar makiya guda.


Juyin musuluncin na Iran ya sauya zuwa gwamnati da tsari na tafiyar da mulki. Saboda haka Musulunci ya sake tabbatar da cewa zai iya kafuwa da tafiyar da rayuwar al’umma a cikin kowane zamani. Kuma hakan ya rusa parpaganda ta shekara da shekaru  da yammacin turai su ka rika yi akan addinin Musulunci na bayyana shi a matsayin wani wanda bai dace da zamani ba.


Juyin Musulunci na Iran wanda ya gaskata kansa cewa zai iya, ya cusawa al’ummar kasar son ‘yanci da riko da shi da daukaka da kuma adalci. Daga nan ne kuma ya watsu zuwa kasashen musulmi musamman ma dai al’ummun da ake zalunta. Kuma saboda al’ummar musulmi tana kunshe da al’adu daban-daban a cikinta wadanda su ke rayuwa cikin fahimtar juna saboda riko da Musulunci, ya sa sun sami wani karfi na jin cewa suna da abin fada a fagen siyasar kasa da kasa. Za kuma su iya taka rawa a fagage da su ka suka shafi kare hakkin bil’adama da girmama mutum bisa kasantuwarsa mutum mai kima da daraja.


Kasashen mulkin mallaka da masu takama da karfi a duniya ba son su ba ne, a ce an sami fahimtar juna a tsakanin kasashen wannan yankin. Abinda juyin Musulunci na Iran ya yi imani da shi, shi ne cewa, wajibi ne a karfafa rawar da addinin Musulunci ya ke takawa wajen daukar duk wasu matakai afagage daban-daban na rayuwa. Haka nan kin amincewa da siyasar nuna karfi na manyan kasashe. Sai kuma bai wa kasashe damar su zama masu daukar makomarsu.


 Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi imani da cewa gina alaka mai karfi a tsakanin kasashen yanki da kuma na kasashen musulmi yana da matukar muhimmanci wajen kare manufofin al’ummar musulmi da kuma hana afkuwar rikici da fadace-fadace a tsakaninsu.


Idan kuwa har akwai wannan irin alakar a tsakanin kasashen musulmin da na wannan yankin, to shakka babu zai karfafa matsayar da al’ummar musulmi su ke da shi baki daya a fagen siyasar duniya. Kuma dole ne ya zama sai da su za a rika daukar matakai wajen tafiyar da al’amurran duniya.


A hakikanin gaskiya, tsarin jamhuriyar Musulunci ta Iran yana karfafa wajabcin a rika girmama hakkokin al’ummu da kuma yin mu’amala da su da kuma hulda bisa adalci.


 Bugu da kari, wani fage da tsarin jamhuriyar Musulunci ta Iran ya yi aiki akansa shi ne karafafa dankon zumunci a tsakanin kasashen musulmi da wadanda ba na musulmi ba, bisa dogaro da abubuwa masu kima da su ka yi tarayya akansu. Wadannan abubuwan masu kima sun kunshi fada da wairya da nuna banbanci da son shimfida adalci da fada da zalunci na kasashe masu takama da karfi. Haka nan kira zuwa ga shimfida tsarin adalci na al’umma.


Saboda wannan matakin da matsayin na  juyin Musulunci ta Iran, ne Amurka da ‘yan sahayoniya su ke adawa da tsarin Musulunci na Iran. Suna daukarta a matsayin barazana a gare su.


 


Feb 07, 2016 07:29 UTC
Ra'ayi