• Mahangar Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Akan Take Hakkin Bil'adama A Iran ( 1)

Amfanin Da Ma'anoni Masu Kima Domin Shiga Harkokin Cikin Gidan Wasu Kasashe

Sanannen abu ne cewa ma aikatar harkokin wajen Amurka ta gina ayyukanta ne akan tafka laifuka akan bil'adama. Amma kuma a lokaci guda wannan kasar ce ta ke fitar da bayani akan take hakkin bil'ama a cikin kasashen duniya daban-daban. Babu tantama Amurka ce akan gaba wajen laifukan da aka tafka akan bil'adama. Za kuwa a iya ganin wanann danyen aikin na Amurka a cikin yake-yaken da tayi kai tsaye da wadanda ta yi ta bayan fage. Daga ciki da akwai yakin da ta kallafawa Iran ta hanyar Iraki na tsawon shekaru 8. Ita ce ta rika bai wa Irakin tallafi makamai da bayana na asiri a tsawon shekarun yakin.

Shekaru masu tsawo Amurka da kawayenta suka dauka suna kokarin damfarawa duniya nuna karfi ta hanyar amfani da wasu ma'anoni masu dadin fada, kamar kare hakkin bil'adama. Suna bayyana kawukansu a matsayin masu kare hakkin bil'adama, saboda haka su ke halartawa kawukansu tsoma baki a harkokin wasu kasashe da ma amfani da karfi.

 

Amurkan da kawayenta sun kasa mutanen duniya zuwa gida-gida tsakanin masu daraja ta farko da ta biyu zuwa ta uku.

A mahnagar kasashen yammacin turai mutanen Asiya da Afirka da yankin Latin na Amurka, suna a matsayin masu daraja ta biyu da uku ne. Amurkan da turawan yamma su ne masu daraja ta farko. A dalilin haka tsaron kasar Amurka da na turai ne mai muhimmanci, yayinda tsaron sauran kasashen duniya ba shi da wani muhimmanci.

Hatta batun azabtarwa da kuma ayyukan ta'addanci, halartacce ne idan su da kawayensu h.k. Isra'ila ne su ka aikata.

 

Wanann irin tunanin karkatacce ne da Amurkan ta ke da shi, ta ingiza Sadam ya yaki Iran, sannna kuma ta kau da ido a lokacin da ya yi amfani da makami mai guba akan al'ummar Iran da Kurdawa. Fiye da mutane 100,000 ne su ka rasa rayukansu a sanadiyyar wancan harin na Sadam. Wasu dubban kuma su ka zama marasa lafiyar da har mutuwarsu suna cikin radadi da azaba.

Gabanin harin da Saddam din ya kai a garin Sardasht, Kasashen da su ka yi amfani da makami mai guba su ne wadanda su ka shiga yakin duniya na farko. Sai kuma ita kanta Amurka a lokacin yakin Vietnem.

 

A vietnem, Amurka ta watsa gubar da ta kai lita miliyan 800 a kan mutane da dabbobi da gonaki.

Wasu bayanai na bayan nan ma sun tabbatar da cewa Saddam ya sami makamana masu guba ne daga kasashen turai da Amurka.

Kamfanonin kasashen Jamus da Hollanda da Faransa da Belgium da Rasha da Amurka sun taka rawa wajen samarwa da Sadam din makamai masu guba. Ashe wannan baya nuni da wadanda su ke take hakkin bil'adama?

Wani kwararre a fagen harkokin tsaro mai suna Gordon Dove, ya bayyana cewa; Amurka tana da hannu a cikin laifukan yakin da Saddam ya tafka. Musamman a harin makamai masu guba akan Iran.

Gordov wanda shi kanshi tsohon sojan Amurka ne da ya yi yakin Vietnem ya bayyana cewa; Daya daga cikin dalilan kai wa Iraki hari a 2003 shi ne; yin amfani da makamai da aka sirka su da sanadarin Urani'um. Makamai ne wadanda sannu a hankali illarsu ta rika fitowa fili acikin al'ummar Iraki.

Gordov ya kuma ce; Amurka ce kasar da a kodayaushe take nuna cewa ita mai kare hakkokin bil'adama ce,amma kuma alokaci guda tana kai wa kasashe hari. Ita ce kuma ta ke riya cewa tana kare yancin tofa albarkacin baki da tsarin demokradiyya, alhaki ta ke yakar kasashe.

 

Har ila yau, Gordov ya ce; Da akwai wasu kwararan bayanai da suke nuni da tabbatar da cewa Amurkan tana da kamfanoni na kera makamai masu guba da sunan na bincike da nazarin ayyukna gona a cikin kasashen Goergia da Bulgaria da Qazakistan da Ukrania. Wasu kamfanonin kuma an kafa su ne da sunan nazarin aikin likitanci.

Sai dai a duk lokacin da aka sami wadanda su ka fito da bayanai akan hakikanin abinda wani kamfani ya ke yi, sai a sauya masa kasa. Su kuma ci gaba da gudanar da ayyukan da su ke yi.

 

A mahangar manyan kasashen duniya, mallakar makamai masu guba da za su basu fifito na karfi, wani abin nema ne. Koda kuwa wadannan makaman za su yi sanadin mutuwar dubban mutane a cikin kankanen lokaci.

Wannan kuwa shi ne hakikanin take hakkin bil'adama.

Hatta akan batun makaman Nukiliya, haka nan tunanin Amurkan da wasu kasashen turawan yake. Amurka ce ta kirkiri akidar da ke cewa; Kera Bom domin Sulhu" a 1950; ayanzu da aka shiga cikin karni na 21 ita ce ta farko wajen yawan makaman Nukiliya a duniya.

Kididdiga ta tabbtar da cewa da waki makaman Nukiliya 16,000 a cikin kasashe 9, sai dai kaso 90% na wadannan makaman mallakin Amurka ne da Rasha.

Kuma da akwai makamai masu alaka da Nukiliyar da aka girke cikin shirin a harba su, har guda 18,000. Kuma mafi yawancin wadannan makaman sun fi wadanda Amurkan ta yi amfani da su a Heroshima da Nagasaki karfi da barna.

 

A shekarar 2009 shugaban Amurka Barrack Obama ya rika bada taken kawar da makaman Nukiliya daga doron kasa, sai dai a yanzu da mulkinsa ya zo karshe, babu wani abu da ya sauya.

Mai makon hakan ma, Amurkan ta na ci gaba da aiwatar da shirinta na sabunta makamanta na nukiliya duk bayan shekaru 25.

 

 

 

 

Jun 25, 2016 14:29 UTC
Ra'ayi