Feb 02, 2016 13:58 UTC
  • Fara aiwatar da yarjejeniyar nukiliya
    Fara aiwatar da yarjejeniyar nukiliya

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Iran A Mako shi ne da ke leko muku wasu daga cikin muhimman al’amurran da suka faru a Iran cikin mako wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi a kowane mako.

Kamar yadda muka saba ga wasu daga cikin lamurran da suka faru din kana daga baya mu yi dubi cikinsu.

Daga cikin lamurran da suka faru cikin makon ko shakka babu har da batun da ya shafi fara aiwatar da yarjejeniyar aiki tare da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya lamarin da ya kai ga dage wa Iran din takunkumin da aka sanya mata. Za mu yi dubi cikin wannan lamarin da kuma irin yadda kasashen duniya suka faru isowa Iran din don cimma yarjejeniyoyi na kasuwanci da sauransu. Har ila yau kuma a bangaren da ya shafi takunkumin ma dai a cikin makon ne Amurka ta sanar da sake sanya wa Iran wani sabon takunkumin bayan dauke wasu da ta yi shi ma dai za mu yi dubi cikin hakan da kuma irin martanin da jami’an Iran suka yi. Har ila yau a cikin makon ne kuma dai shugaban kasar China ya kawo ziyarar aiki na Iran inda ya gana da manyan jami’an kasar ciki har da Jagoran juyin juya halin Musulunci inda Jagoran yayi karin bayani kan batutuwa daban-daban musamman siyasar Amurka. Kamar yadda kuma a cikin makon ne dai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jinjinawa sojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci saboda kame sojojin Amurka masu wuce gona da iri da suka yi.

Wadannan watakila da ma wasunsu suna daga cikin batutuwan da za mu yi dubi cikin shirin na mu na yau. Sai a biyo mu sannu a hankali.

--------------------------------/

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin a cikin makon da ya wuce ne aka fara aiwatar da yarjejeniyar aiki tare da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya na kungiyar 5+1 dangane da shirin nukiliyan zaman lafiya na Iran din, lamarin da ya sanya aka dage mata dukkanin takunkumin da aka sanya mata da suke da alaka da shirin nukiliyan nata da suka hada da wadanda kwamitin tsaron MDD ya sanya mata da kuma na kungiyar Tarayyar Turai bugu da kari kan wadanda Amurka ta sanya mata.

Sama da shekaru goma kenan dai kasashen yammaci suka kirkiro wannan rikici kan shirin nukliyar kasar Iran lamarin da ya kai ga sanya wa kasar takunkumi kala-dakala. Amma bayan tattaunawa na fiye da shekaru biyu kasashe masu kujerun din din din a kwamitin tsaron MDD wato Amurka, Rasha, China, Faransa da kuma Britania hada da kasar Jamus sun cimma matsaya kan yadda za a kawo karshen wannan rikicin, lamarin da Iran ta amince shi matukar dai zai kare matsa hakkin da take da shin a mallakar fasahar nukiliyan. Daga karshe dai an cimma matsayar cewa Iran za ta takaita wasu bangarori na shirin nukiliyan nata sannan su kuma wadannan kasashen a na su bangaren za su dage mata takunkuman tattalin arzikin da suka dora mata. An fara aiwatar da wannan yarjejeniyar a ranar 17 ga watan Janairun nan bayan da shugaban hukumar IAEA Yokiyo Amano ya gabatar da rahotonsa da ke tabbatar da cewa Iran ta aiwatar da dukkan sharuddan da ta amince da su a yerjejeniyar da ta cimma.

A wata ganawa da suka yi da manema labarai ministan harkokin wajen Iran Mohammad Jawad Zarif da takwararsa ta Tarayyar Turai Federica Mogherini suka sanar da duniya dagewa Iran dukkan takunkuman da aka dora mata wadanda suke da dangantaka da kan shirinta na makamashin nuklia kamar yadda yerjejeniyar da suka cimma da ita a cikin watan yulin shekarar da ta gabata ta zayyana.

Wannan sanarwar dai ta fuskanci maraba daga kusan dukkanin kasashen duniya in ban da ‘yan wasu tsirarru wadanda dukkanin makirce-makircen da suka kulla wajen ganin ba a dage wa Iran takunkumin ba suka ci tura. Dage wadannan takunkumin dai ya share fagen da kamfanoni na kasashe da kuma na ‘yan kasuwa fara shirye-shiryen zuwa Iran din don kulla yarjejeniyoyi na kasuwanci da za su amfani dukkanin bangarorin biyu.

----------------------------------/

A ci gaba da share fagen aiki tare da kulla alakoki na tattalin arziki tsakanin Iran da sauran kasashen duniya bayan dage takunkumin ne, a farko farkon wannan makon ne shugaban kasar China Xi Jinping ya kawo ziyarar aiki nan Iran don inda ya gana da manyan jami’an kasar ciki har da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei da shugaban kasa Hasan Ruhani da sauran manyan jami’an kasar ta Iran inda bangarori biyu suka sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi na kasuwanci da al’adu da tsaro da sauransu a tsakaninsu.

A ganawar da yayi da shugaban kasar Chinan, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana jin dadinsa da irin kyakkyawar alakar da ke tsaknin Iran da China inda ya ce ko da wasa Iran ba za ta taba mancewa da irin kyakkyawar mu’amalar da China ta yi da ita a zamanin takunkumi din ba.

Yayin da yake magana kan siyasar Amurka a yankin Gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana siyasar Amurka a matsayin wata siyasa ta yaudara da rashin gaskiya, don haka sai ya yi kiran da a samu karfafuwar alaka tsakanin kasashen duniya ma'abota 'yancin kai.

 

Har ila yau Jagoran ya bayyana ikirarin Amurkawa na kafa ‘Hadakar Fada da Ta’addanci’ a matsayin wata yaudara kawai yana mai cewa: Wannan ita ce siyasar Amurka cikin dukkanin lamurra. Babu wani lokaci da suke nuna gaskiya cikin mu’amalarsu.

Har ila yau kuma yayin da yake ishara da maganar shugaban kasar China dangane da batun karfafa alaka ta tsaro tsakanin kasashen biyu, Jagoran ya bayyana cewar: Abin bakin cikin shi ne cewa irin bakar siyasar kuskure ta kasashen yammaci haka nan kuma da irin gurguwar fahimtar da wasu suka yi wa Musulunci, sun sanya yankin gabas ta tsakiya fuskantar matsalar rashin tsaro Don haka sai ya ce wajibi ne a yi amfani da hikima da hada kai waje guda don fada da hakan.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana wasu kasashen wannan yankin a matsayin tushen bayyanar irin wadannan gurbatattun tunani inda ya ce: Su kuma kasashen yammaci maimakon su yi fada da tushe na asali na wannan tunani da kuma kungiyoyin ta’addanci, sai suka koma kan musulman da suke Turai da Amurka da kuma ci gaba da matsa musu lamba, alhali kuwa wadannan kungiyoyi na ta’addanci sun yi hannun riga da ingantacciyar akida kuma tunani na Musulunci.

 

Shi ma a nasa bangaren shugaban kasar China Xi Jinping, ya bayyana aniyar kasarsa ta ci gaba da fadada alakarta da kasar Iran a dukkanin bangarori da suka hada da al'adu, ilimi, fasaha, tattalin arziki, tsaro da kuma fada da ta'addanci.

------------------------------------/

Masu saurarare barkanmu da sake saduwa.

Har ya zuwa yanzu batun kama sojojin ruwan Amurka da sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci suka yi a lokacin da suka shigo cikin ruwan Iran ba tare da izini ba, yana daga cikin batutuwan da suke ci gaba da jan hankula da kuma karin bayani da dakarun na Iran suke ci gaba da yi dangane da hakikanin abin da ya faru.

A saboda haka ne ma a ranar Lahadin da ta gabata ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da matasa sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran wadanda suka nuna jaruntaka wajen kame sojojin ruwan Amurka masu wuce gona da iri da suka shigo cikin ruwan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba tare da izini ba, inda Jagoran ya jinjina da kuma gode musu kan wannan jaruntaka da suka nuna.

A gajeren jawabin da yayi musu a yayin wannan ganawar, Ayatullah Khamenei ya bayyana wannan aiki da sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musuluncin suka yi da cewa wani aiki ne na jaruntaka da ke cike da imani, daga nan sai ya ce: Wannan aiki naku yayi kyau sosai sannan kuma kun yi shi a daidai lokacin da ya dace. A hakikanin gaskiya wajibi ne a dauki abin da ya farun a matsayin wani aiki na Ubangiji, wanda ya janyo Amurkawa cikin ruwan kasar mu, don ku sami damar kama su a irin wannan yanayi, hannayensu a kan kawunansu.

Tun dai bayan faruwar wannan lamarin al’ummar Iran suke ci gaba da jinjinawa dakarun kare juyin juya halin Musuluncin saboda wannan jaruntaka da suka nuna wajen kare kasar Iran daga dukkanin wata barazana da kasar za ta iya fuskanta daga wajen makiya; lamarin da ya sanya Jagoran juyin juya halin Musulunci ma a jawabin da ya yi a kwanakin baya ya kirayi sauran jami’an kasar da su yi koyi da wadannan matasan wajen kare hakkoki da kuma mutumcin Iran daga dukkanin wuce gona da iri na makiya.

------------------------------------/

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin jami’an Iran daban-daban suna ci gaba da mai da martani ga sanarwar da gwamnatin Amurka ta yi na sake sanya wa Iran sabon takunkumi saboda gwajin makamai masu linzami da ta yi.

A wata hira da yayi da tashar talabijin din CNN ta kasar Amurka, ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya kirayi Amurka da ta sake dubi cikin siyasarta musamman siyasar ci gaba da sanya wa Iran takunkumi wanda har ya zuwa yanzu ta gaza kai ta ga abin da abin da take fatan gani, wato durkusar da Iran da kuma mai she ta 'yar amshin shatan ta.

Minista Zarif yana mai da martani ne dangane da sabon takunkumin da gwamnatin Amurka ta kakaba wa Iran kwana guda bayan dage wasu takunkumin da ta yi sakamakon fara aiwatar da yarjejeniyar nukiliya da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya. Ministan harkokin wajen na Iran ya kwatanta wannan dabi'a ta gwamnatin Amurka da mutumin da ya kamu da shan taba, duk da cewa ya san babu wani amfani da yake samu daga shan tabar in ban da cutarwa, amma dai ya gagara bari don ta zamanto masa jaraba. Don haka sai ya kirayi 'yan siyasar Amurka da cewa ya zama wajibi gwamnatin Amurka ta samar wa kanta wani yanayi na yarda da cewa takunkumi dai ba zai haifar mata da da mai ido ba a kan Iran, tattaunawa da girmama juna ita ce kawai mafita a gare ta.

 

Ko shakka babu, Amurka ta san cewa Iran ko da wasa ba ta taba zama barazana ba ga yankin da ma duniya baki daya, don kuwa sama da shekaru 36 kenan da nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran amma babu wani lokaci da Iran ta taba barazana ko kuma kai hari kan wata kasa a duniyar nan, duk kuwa da barazanar da ta fuskanta kuma take ci gaba da fuskanta kai tsaye ko kuma ta wata hanya ta daban daga wasu kasashen, ciki kuwa har da yakin shekaru 8 da aka kallafa mata bugu da kari kan makirce-makircen kifar da gwamnatin kasar da kuma ayyukan ta'addanci daban-daban da kasar ta fuskanta kuma take ci gaba da fuskanta. Baya ga cutarwa ta tattalin arziki da ta fuskanta daga wasu daga cikin kasashen da suke makwabta da ita da dai sauransu.

 

Kamar yadda a fili yake cewa gwajin makamai masu linzami da Iran ta yi wanda shi ne gwamnatin Amurka ta fake da shi wajen sake sanya mata wannan sabon takunkumin, wani shiri ne wanda yake a matsayin shirin kare kai da kowace take yi don kare kasa da kuma al'ummarta wanda kuma ba shi da wata alaka da batun kera makaman nukiliya. Ana iya cewa Iran tana daga cikin kasashen da a kullum suke fuskantar barazana kawo mata hari daga wajen manyan kasashe ma'abota girman kan duniya da kuma wasu kasashen da suke makwabtaka da ita biyagoyon baya da kuma taimakon manyan kasashen duniyan karkashin jagorancin Amurka lamarin da ya tilasta mata yin dukkanin abin da za ta iya wajen kare kanta. To sai dai kamar yadda jami'an kasar suka sha fadi kuma har fatawa ma Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar ya fitar kan haramcin kerawa da kuma ajiye makaman kare dangi.

Don haka ne jami'an Iran din suke ganin sanya takunkumi wa Iran saboda shirin makamai masu linzami, tamkar takunkumi daban-daban da aka sanya mata saboda shirin nukiliyanta na zaman lafiya, takunkumi ne da suka saba wa doka kuma ba za su haifar da da mai ido ba ga masu sanya shi. Watakila ana iya sanya hakan ne cikin sahun abin da ministan harkokin wajen na Iran ya siffanta da cewa Amurka dai ta jarabtu da sanya takunkumi ne ko da kuwa ta san babu wani amfani da zai mata, kamar yadda mai shan tabar da ta zamanto masa jaraba, zai ci gaba da sha ne ba wai saboda tana amfanar da shi ba.

--------------------------------------/

END


Tags

Ra'ayi