Feb 02, 2016 14:32 UTC
  • Azadi square
    Azadi square

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Iran A Mako da ke leko muku wasu daga cikin muhimman al’amurran da suka faru a Iran cikin mako wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi, da fatan masu saurare suna cikin koshin lafiya.

Kamar yadda muka saba ga wasu daga cikin muhimman al’amurran da suka farun kana mu yi karin haske kansu daga baya.

 

Ko shakka babu bikin cika shekaru 36 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran shi ne kan gaban batutuwan da suka fi daukar hankula a kasar. Don haka wannan shi ne batun da za mu fi ba shi muhimmanci a shirin na mu na yau da kuma irin abubuwan da aka gudanar. Har ila yau kuma za mu yi dubi cikin batun wasikar da wasu kafafen watsa labaran Amurka suka yi na cewa Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya aike wa shugaban Amurka da wasika da kuma lamurran da suka gudana a fagen diplomasiyya cikin mako a nan Iran.

 

Sai a biyo mu bayan wannan mabudin kunnen don jin yadda shirin zai kasance.

 

---------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

A ranar Larabar da ta gabata ce wacce ta yi daidai da ranar da juyin juya halin Musulunci na kasar Iran ya yi nasara a ranar 11 ga watan Fabrairun 1979 aka gudanar da bukukuwan tunawa da nasarar juyin juya halin Musuluncin a duk fadin Iran inda al’ummar Iran suka sake jaddada irin hadin kai da kuma goyon bayan da suke ba wa juyin tsawon shekaru 36 da suka gabata.

 

Kamar kowace shekara miliyoyin al’ummar Iran din a duk fadin kasar suka fito kan titunan birane da kauyukansu don nuna godiyarsu ga Allah Madaukakin Sarki bisa wannan ni’ima da ya yi musu na samun wannan juyi da kuma sake jaddada mubaya’arsu ga marigayi Imam Khumaini (r.a) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma jagora Imam Khamenei.

 

Ko shakka babu wannan tana ta 22 ga watan Bahman rana ce mai tsohon tarihi kana kuma wacce duniya, masoya da kuma makiyan juyin, suke zuba ido su ga abin da al’ummar Iran din za su yi da kuma matsayarsu kan juyin juya halin Musuluncin na su. Su dai makiyan dai fatansu da kuma dukkanin kokarin da suke yi shi ne kashe wa mutanen Iran din gwiwa don kada su fito zanga-zangar da ake gudanarwa a wannan rana don su sami damar farfaganda da nuna wa duniya cewa al’ummar Iran su kosa da juyin. To sai dai kuma kamar kowace shekara al’ummar Iran din sun bada musu kasa a fuska sakamakon gagarumin fitowar da suka yi wacce an yi imani ta ma dara na shekarar da ta gabata.

 

Da dama daga cikin kafofin watsa labaran duniya sun watsa bukukuwan da aka gudanar din da kuma wannan jerin gwanon na al’umma wasu ma kai tsaye musamman jawabin da shugaban kasar ta Iran Dakta Hasan Ruhani ya yi a wajen bikin; musamman bangaren da ya yi magana kan shirin nukiliyan zaman lafiya na Iran da kuma tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da manyan kasashen duniya kan wannan shirin, inda shugaba Ruhanin yayi watsi da ikirarin da wasu jami’an Turai da Amurka suke yi na cewa matsin lamba da kuma takunkumin da aka sanya wa Iran shi ne babban dalilin da ya sanya ta amincewa ta zauna teburin tattaunawa da turawan lamarin da shugaban ya ce karya ce kawai tsagoronta.

 

Ko shakka babu irin fitowar da al’ummar Iran suka yi kwansu da kwarkwatarsu ciki kuwa har da manyan jami’an gwamnatin kasar a yayin jerin gwanon da aka gudanar din wani lamari ne da ke nuni da azamar da suke da ita na ci gaba da goyon bayan juyin na su da kuma tabbatar wa da duniya cewa lalle ba za su taba mika wuya da matsin lamban turawan ba ko kuma kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana da cewa fitowar al’umma wani mayar da martani ne mai kaskantarwa ga masu adawa da kasar ta Iran.

 

--------------------------------------------/

 

Daga cikin bukukuwan da aka gudanar a wannan shekarar har da wani wani taron kara wa juna sani don kusato da ra’ayi da fahimtar al’ummomi kusa tsakanin baki mahalarta taron cikon shekaru 36 da samun nasarar juyin juya halin Musuluncin.

 

Shi dai wannan taro wanda ya sami halartar baki 460 daga kasashe 38 na duniya da suka hada da masana da ‘yan jaridu daban-daban na duniyar an gudanar da shi ne a nan birnin Tehran.

 

Kamar yadda kuma an gudanar da wani taron na daban na ‘yan jaridu da marubutana kasashen duniya wanda shi kuma aka gudanar da shi a garin Isfahan daya daga cikin manyan biranen kasar ta Iran.

 

Taken wannan taron dai shi ne ‘Tasirin da sahyoniyawa suke da shi cikin kafafen watsa labaran Amurka’

 

A jawabin da ta gabatar a wajen taron, sananniyar ‘yar jaridar nan kuma tsohuwar ‘yar majalisar Amurka Alisson Weir ta yi ishara da irin tasirin sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya aike wa matasan Amurka da Turai a kwanakin baya inda ya ce wani adadi mai yawan gaske na matasan Amurka da Turai din sun karanta wannan sako sannan kuma yayi musu gagarumin tasiri.

 

Haka nan kuma yayin da take ishara da irin tasirin da sahyoniyawa suke da shi cikin kafafen watsa labaran Amurka wani lamari ne da ke a fili, tana mai cewa ko shakka babu daliban jami’oin wadannan kasashe na yammacin turai sun fahimci wanann sako na Jagora da ke kokarin wayar musu da kai daga irin gurbata hakika da kafafen watsa labaran suke yi.

 

---------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Wani lamari da ya dau hankula a ciki wa da wajen Iran shi ne labarin da jaridar Wall Street Journal ta Amurka ta buga inda ta yi ikirarin cewa Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya aike wa shugaban kasar Amurka da wata wasika a asirce a ci gaba da tattaunawar da Iran take yi da Amurka kan shirin nukiliyanta na zaman lafiya.

 

Wannan labarin dai ya janyo hankula inda kafafen watsa labarai da masana daban-daban na duniya suka kawo shi da kuma yin sharhi kansa musamman.

 

To sai dai kuma wani lamarin da ya kara janyo hankula kan wannan lamarin shi ne musanta wannan labari da Iran ta yi na cewa babu wani abu makamancin hakan, wato Jagoran juyin juya halin Musuluncin bai aike wa Obama da wata wasika ba.

 

Ma’aikatar harkokin wajen Iran, ta bakin mai magana da yawunta, Malama Marzieh Afkham ce ta musanta wannan labarin da kuam yin watsai da shi don kuwa ba shi da tushe tana mai cewa hakan wani kokari ne na wasa da hankula da kafafen watsa labaran suka saba.

 

Malam Afkham ta ce: A baya dai shugaban Amurka ya sha rubuto wasika zuwa nan Iran, inda a wasu lokuta a kan ba shi amsa. Sai dai tace cikin ‘yan kwanakin baya-bayan nan babu wata wasika da aka aike wa shugaban Amurkan kamar yadda jaridar ta yi ikirari.

 

-------------------------------------./

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

A bangaren diplomasiyya kuma, a cikin makon ne ministan harkokin wajen kasar China Wang Yi ya kawo ziyarar aiki na kwanaki biyu nan Iran don ganawa da manyan jami’an kasar dangane da alakar da ke tsakanin kasashen biyu, bugu da kari kan lamurra da suka shafi kasa da kasa da kuma wannan yanki na Gabas ta tsakiya.

 

Daga cikin jami’an da ministan harkokin wajen na China ya gana da su, baya ga takwararsa na Iran Dakta Jawad Zarif, har da shugaban kasa Dakta Hasan Ruhani. A yayin wannan ganawar, shugaba Ruhani yayi ishara da muhimmancin da ke cikin karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu inda ya ce: Tun farko China tana da alaka kyakkyawa da Iran, a halin yanzu kuma kasashen biyu sun kai wani matsayi da fahimtar juna da kuma aiki tare a tsakaninsu da ya kamata a ci gaba da kiyaye shi.

 

Dangane da batun nukiliyan kasar ta Iran kuwa, shugaba Ruhani ya ce matukar dai akwai irada ta siyasa, to kuwa za a iya magance matsalar nukiliyan ta Iran

 

Shi ma a nasa bangaren ministan harkokin wajen na China ya ce kasarsa ta kuduri aniyar karfafa alakarta da Iran ta dukkanin bangarori; kamar yadda kuma ya sake jaddada muhimmancin ci gaba da tattaunawa kan matsalar nukiliya ta Iran da kuma sake nuna rashin amincewar China kan takunkumin da aka sanya wa Iran.

 

----------------------------------------/

 

Har ila yau a fagen kasa da kasa din ma dai a cikin makon ne mataimakiyar shugaban kasar Iran kan harkokin mata da iyali Malama Maulawardi ta kai wata ziyara ta kwanaki uku zuwa fadar Vatican da ke birnin Roma na kasar Italiya inda ta gana da Paparoma Francis, shugaban mabiya darikar Katolika ta duniya.

 

Har ila yau kuma a yayin ziyarar dai malama Maulawardi ta gana da Cardinal Pietro Parolin, firayi ministan fadar ta Vatican bugu da kari sauran manyan jami’ai da malaman fadar ta Vatican.

 

Mataimakin shugaban na Iran dai ta kai wannan ziyarar ne bisa gayyatar da fadar Vatican din ta yi mata.

 

A ganawar da ta yi da Paparoma Francis din, bangarori biyun sun bayyana wajibcin tattaunawa tsakanin addinai musamman tsakanin addinin Musulunci da addinin Kirista don ciyar da manufocin da suka yi tarayyar cikinsu gaba.

 

Kamar yadda kuma bangarori biyu suka tattauna kan matsalolin da suka shafi mata da sauransu.

 

-----------------------------------------/

 

END

Ra'ayi