Feb 27, 2016 07:42 UTC

Jama’a masu saurare AssalamuAlaikum barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da kua cikin wannan shiri an Afirka a mako.

Jama’a masu saurare AssalamuAlaikum barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da kua  cikin wannan shiri an Afirka a mako, Shirin kan yi dubi kan wasu daga cikin muhimman batutuwa da suka danganci kasshen anhiyar Afirka, nda a yau za mu leka tarayyar najeriya, J. Nijar, Uganda da kuma Libya, da ma wasu batutuwan na daban gwargwadon yadda lokaci ya bamu hali.
Da fatan za a kasance tare da mua  cikin shirin.
Music………………………………..
To madalla, bari mu fara shirin daga kasar Uganda, inda a ranar Lahadin da ta gabata ce jami’an tsaron kasar suka kame Dr. Kizza Besigye, dan takarar babbar jam’iyyar adawa a kasar ta Uganda, a zaben da za a gudanar a kasar, inda zai kara da shugaba Yoweri Museveni, wanda ya kwashe tsawon shekaru 30 a jere yana mulkin kasar ta Uganda.
Jami’an tsaron na gwamnatin Uganda sun lakada ma madugun adawar dan Karen duka tare da magoya bayansa, a lokacin da suke gudanar da wani rali a cikin birnin kampala a cikin jerin gwanon dubban motoci, sun kuma tsare shin a wasu ‘yan sa’oi.
Jami’an tsaron sun ce sun dauki wannan matakin kan jagoran ‘yan adawar ne saboda ya tare hanyoyi a cikin babban birnin kasar.
……………………………..
To a can tarrayyar Najeriya kuwa, batun korar wasu manyan aikatan gwamnati a cikin wannan mako shi ne ya fi daukar hankali, inda Segun Adeyemi, kakakin ministan watsa labarai, Alhaji Lai Mohammed, ya fara fitar da wata sanarwa a ranar Litinin da ke cewa, an kori shugabannin gidan talabijin na gwamnatin tarayya, (NTA), da Federal Radio Corporation of Nigeria (FRCN), da muryar Najeriya, da kamfanin dillacin labarai na kasar (NAN), da hukumar sa idanu a kan kafafen watsa labarai na kasar da hukumar wayar da kan jama'a ta kasar (NOA).
Daga bisani kuma wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban kasar, wadda ta sanar da korar shugabannin wasu ma'aikatu 20 na daban.
……………………………………..
To a jamhuriyar Nijar kuwa batun bayar da sheda kan masu zabe ba tare da takardu ba wanda hukumar zaben kasar ta amince da shi matukar dai an amince da su ‘yan kasa ne, yana daga cikina bin da ke ci gaba da daukar hankali, yayin da su kuma yan adawar kasar suka yi watsi da wannan batu, inda suke zargin cewa wani sabon salo ne na magudi aka bullo da shi a kasar a hukumance.
………………………………..
A cikin wannan mako ne shugaban kasar Somalia ya bayyana cewa mayakan Boko Haram suna samun horo daga hannun takwarorinsu na Alshabab a Somalia, kafin daga bisani su nufi Najeriya da sauran kasashen da suke kai hare-hare, wanda kuma masana kan harkokin saro suna kallon wannan furuci da fuskoki daban-daban.
……………………………………
A can kasar Kamaru kuwa a ranar 11 ga wannan wata ne aka gudanar da tarukan ranar matasa d ake gudanarwa a kasar a kowace shekara a karo na 50.
………………………………………………
Dangane da badakalar da ake ciki a kasar Libya kuwa, bangarorin siyasa sun cimma matsaya kan batun kafa gwamnati da za ta hada dukkanin bangarorin kasar, da suka hada yan siyasa da kuma kabilu har ma da wasu daga cikin yan tawaye da suke dauke da makamai, yayin da wasu kungiyoyin musamman wadsanda suke da alaka da ISIS ko alkaida ba su amince da hakan ba. A kan wannan yunkuri na siyasa a Libya
…………………………..
To jama’a lokacin da muke da shi ya kawo jiki a na zamu dakata sai Allah ya kai mu mako na gaba za a ji mu dauke da wani shirin, kafin lokacin nake yi muku fatan alkhairi, wassalamu alaikum wa rahmatullah.Tags

Ra'ayi