Feb 02, 2016 14:34 UTC
  • taron yarjejeniyar nukiliya
    taron yarjejeniyar nukiliya

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Iran A Mako da ke leko muku wasu daga cikin muhimman al’amurran da suka faru a Iran cikin mako wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi a kowane mako da fatan masu saurare suna cikin koshin lafiya.

Yau ma ga mu da wani sabon shirin, amma kafin mu je ga cikakken shirin ga wasu daga cikin kanun labaran da za ku ji.

 

Daga cikin batutuwan da suka dau hankula cikin makon har da ganawar da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi da mutanen lardin Azarbaijan ta Gabas don tunawa da yunkurin mutanen Tabriz a shekarar 1978 wajen tinkarar tsohuwar gwamnatin Shah ta kasar inda ya yi karin haske kan batun takunkumin da aka sanya wa Iran. A bangaren diplomasiyya ma ziyarar da mataimakin shugaban kasar Iran ya kai kasar Iraki da kuma wanda ministan harkokin wajen Iran ya kai ziyara kasashen Azarbaijan da Belarus suna daga cikin batutuwan da suka dau hankula. A fagen shirin nukiliyan zaman lafiya na Iran kuwa daga cikin batutuwan da suka fi daukan hankula shi ne ci gaba da tattaunawar da Iran take yi da manyan kasashen duniya musamman Amurka kan wannan batu inda ministocin harkokin kasashen biyu suka gana da junansu kan wannan batu. Har ila yau kuma sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aike wa matasan Turai da Arewacin Amurka yana ci gaba da daukan hankula inda masana da ‘yan siyasa suke ci gaba da sharhi kansa.

 

Wadannan watakila da ma wasunsu suna daga cikin batutuwan da za mu yi dubi cikinsu, a shirin na mu na yau. Sai a biyo mu sannu a hankali bayan wannan mabudin kunnen.

 

----------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin A karshen makon ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubun dubatan mutanen lardin Azarbaijan ta Gabas da ke arewa masu yammacin kasar Iran don tunawa da yunkurin mutanen garin Tabriz a shekarar 1978 watanni kafin nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran inda jagoran yayi karin haske kan lamurra daban-daban da suka shafi kasar Iran da kuma jinjinwa al’ummar kasar saboda irin gagarumar fitowar da suka yi lokacin jerin gwanon ranar nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar ta Iran.

 

Daya daga cikin muhimman lamurran da Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya tabo cikin jawabin nasa shi ne batun takunkumin da makiya al’ummar Iran musamman Amurka suka sanya wa da nufin dunkufar da al’ummar Iran din inda ya ce: Kasashen yammaci musamman Amurkawa, sun yi amfani da hanyoyi da salo daban-daban wajen yin kafar ungulu ga tattalin arzikin Iran. A halin yanzu shekara da shekaru kenan suka sanya wa Iran takunkumi kuma har ya zuwa yanzu suna ci gaba da hakan ta hanyar fakewa da batun shirin nukiliya.

 

Daga nan sai Jagoran yayi karin haske dangane da hanyoyin daban-daban da za a yi riko da su wajen magance matsalar tattalin arzikin wanda daya daga cikin hanyoyin shi ne tsarin tattalin arziki na dogaro da kai da ya gabatar a shekarun baya sannan kuma gwamnatin kasar take ci gaba da aiwatarwa.

 

Jagoran ya ce:: Matukar dai aka gina tushen tattalin arzikin kasar nan da karfin gaske ta hanyar dogaro da irin karfi na cikin gida da ake da shi, to kuwa takunkumi da faduwar farashin mai ba zai cutar da mu ba da sanya mu cikin damuwa ba.

 

A wani bangare na jawabin nasa Jagoran yayin ishara da manufar makiyan Iran wajen sanya mata takunkumi, inda ya ce:

 

Babbar manufarsu ita ce kaskantar da al'ummar Iran da kuma dakatar da gagarumin kokarin da suke yi wajen kai wa ga ci gaba irin na musulnci. Ni na yi amanna da cewa ko da ma a ce za mu amince da sharuddan da suke so kan batun nukiliyan, duk da hakan ba za su dage wannan takunkumin ba. Don kuwa su din da asalin juyin juya halin Musuluncin ne suke adawa.

 

Daga karshe dai Jagoran ya ce matukar makiyan suka ci gaba da sanya wa al’ummar Iran takunkumi, to kuwa ko shakka babu su ma za su mayar da martanin irin wannan takunkumin da na su takunkumin.

 

------------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin a makon da ya wuce ne mataimakin shugaban kasar Iran na farko Dakta Ishaq Jihangiri ya kai ziyara kasar Iraki don ganawa da manyan jami’an kasar ta Iraki kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu da ma yankin baki daya.

 

A ganawar da ya yi da shugaban kasar Iraki Fu’ad Ma’asum, mataimakin shugaban na Iran ya bayyana cewar: Iran dai tana da kwarewa ainun a fagen gina kasa don haka a shirye take ta gabatar da irin wannan kwarewar ga kasar Iraki da kuma taimakawa wajen sake gina kasar Irakin.

 

Shi ma a nasa bangaren shugaban kasar Irakin ya jinjinawa kokarin da Iran take yi wajen rage dogaro da man fetur a bangaren tattalin arzikinta, yana mai cewa kasar Iraki a shirye take ta yi amfani da wannan kwarewar da Iran take da shi.

 

Har ila yau shugaban na Iraki ya jinjina da kuma godiyarsa dangane da irin taimakon da Iran take ba wa kasar Iraki a fadar da take yi da ‘yan kungiyar ta’addancin nan ta Da’esh (ISIS) inda ya sake jaddada aniyar kasar Iraki wajen ganin kasashen biyu sun ci gaba da aiki tare a fagagen siyasa, tsaro da tattalin arziki wajen magance matsaloli da kalubalen da ke gabansu.

 

Har ila yau kuma a yayin wannan ziyarar, kasashen biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyoyin aiki tare a tsakaninsu.

 

------------------------------------------/

 

Har ila yau a fagen diplomasiyyan dai, a cikin makon ne ministan harkokin wajen Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya kai ziyara kasashen Azarbaijan da Belarus inda ya gana da manyan jami’an kasar don tattaunawa kan batutuwan da suka shafi kasashensu.

 

Dakta Zarif ya fara ziyarar tasa ce da kasar Azarbaijan inda ya gana da shugaban kasar Ilham Aliyof da firayi ministansa inda suka tattauna kan lamurran da suka shafi kasashen biyu musamman a fagen tattalin arziki da kuma siyasa.

 

Akwai kyakkyawar alaka ta tattalin arziki da siyasa a tsakanin Iran da Azarbaijan.

 

A kasar Belarsu ma dai ministan harkokin wajen na Iran ya gana da shugaban kasar Alexander Lokoshinko da firayi ministansa bugu da karin kan ministan harkokin wajen kasar haka nan kuma da shugaban majalisa ta kasar.

 

A karshen ziyarar dai ministan harkokin wajen Belarus din ya bayyana cewa bisa la’akari da kyakkyawar alaka ta tattalin arziki da siyasa da ke tsakanin Iran da Belarus, har ya zuwa yanzu kasar Belarus a shirye take ta yi dukkanin abin da za ta iya wajen kara karfafa wannan alakar.

 

---------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin a daidai lokacin da kafafen watsa labarun turai su ka cika duniya da yin magangnu da su ke nuni da batunci ga addinin Musulunci da musulmi, jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya fitar da sako zuwa ga matasan Turai da Amurka ta Arewa. Sako ne wanda ya kunshi yin kira da dogon nazari mai zurfi akan abubuwan da ake fada akan Musulunci na batunci a cikin kafafen watsa labarun turai. Wannan sako kuwa ya zo ne a daidai lokacin da batuncin da ake yi wa Musulunci da musulmi ya kai koli a musamman bayan abin da ya faru a kasar Faransa. Har ya zuwa yanzu dai masana da ‘yan siyasa a kasashen Turai din da Amurka suna ci gaba da sharhi kan wannan sako na Jagoran saboda irin muhimmancin da yake da shi da kuma abubuwan da ya kumsa.

 

Jagoran dai ya bude sakon nasa ne da cewa: Lamurran baya-bayan nan da suka faru a kasar Faransa da makamantansu a wasu kasashen Yammaci, su ne suka sanya ni ganin ya dace in yi magana da ku kai tsaye. Ina magana da ku ne, Ya ku matasa; ba wai saboda na raina iyayenku ba, face dai sai saboda ku ne manyan gobe, wadanda makomar al'umma da kuma kasarku take hannunsu; sannan kuma saboda ina ganin zukatanku cike suke da neman sanin gaskiya. Haka nan kuma ba wai ina magana ne da ‘yan siyasa da jami'an gwamnatocinku ba ne, don kuwa na yi amanna da cewa da gangan sannan kuma da saninsu suka kawar da siyasarsu daga tafarkin gaskiya da hakika.

 

Magana ta da ku kan Musulunci ne, musamman ma dangane irin abin da ake gabatar muku da shi a matsayin Musuluncin.

 

Tsawon shekaru ashirin din da suka gabata zuwa sama - wato tun daga lokacin rugujewar Tarayyar Sobiyeti - an yi gagarumin kokarin bayyanar da wannan addini mai girma a matsayin wani gagarumin abin tsoro. Abin bakin cikin shi ne cewa irin wannan yanayi na sanya tsoro da kyamar (wannan addini) wani lamari ne mai tsohon tarihi cikin tarihin siyasar kasashen yammaci.

 

Ni dai a nan ba ina so ne in yi magana dangane da ‘irin kyama da tsoratarwa' daban-daban da ya zuwa yanzu aka sanya cikin zukatan al'ummomin kasashen yammaci ba. Idan kuka koma kadan cikin tarihi, za ku ga cewa sabbin marubuta tarihi, sun soki mu'amalar rashin adalci da gaskiya da gwamnatocin yammaci suka yi wa al'ummomi da al'adun duniya. Tarihin Turai da Amurka ya rusunar da kansa cikin kunya saboda bautar da mutane, mulkin mallaka da kuma zaluntar wadanda ba fararen fata da kuma wadanda ba Kiristoci ba da suka yi. Masana da malaman tarihinku suna cikin kunyar irin zubar da jinin da aka yi da sunan addini tsakanin mabiya darikar Katolika da Protestant ko kuma da sunan ‘yan kasanci da kabilanci a yakukuwan duniya na daya da na biyu. Shi kansa hakan wani abin jinjinawa ne.

 

Manufar bijiro da wani bangare na wannan doguwar fehrisa na abubuwan da suka faru, ba ita ce sukar tarihi ba, face dai abin da nake so shi ne ku tambayi masananku shin me ya sa a koda yaushe sai bayan jinkiri na gomomin shekaru ko kuma ma daruruwan shekaru ne lamirin al'ummomin yammaci ya ke farkawa da kuma dawowa cikin hayacinsa? Me ya sa ake damfara lamirin mutane ga abubuwan da suka faru cikin tarihin shekaru aru aru ba batutuwan da suke faruwa a halin yanzu ba? Me ya sa ake kange mutane daga fahimtar lamurra masu muhimmanci irin su hanyoyin mu'amala da al'adu da kuma tunani na Musulunci?

 

Ku da kanku kun san cewa wulakanci da haifar da kiyayya da kirkirar tsoron sauran mutane na boge, suna a matsayin wani fage ne da aka yi tarayya cikinsa wajen haifar da dukkanin irin wadannan zalunci da mummunan amfani da mutane. A halin yanzu ina son tambayarku, shin me ya sa yanzu aka dawo da tsohuwar siyasar sanya tsoro da kyamar Musulunci da musulmi? Me ya sa tsarin mulki na duniya a halin yanzu ya sanya tunani na Musulunci a gaba? Shin wasu abubuwa ne da suke cikin tunani da koyarwar Musulunci da har zai zamanto kafar ungulu ga tsare-tsare da siyasar manyan kasashen duniya, sannan kuma me za su samu wajen bakanta fuskar Musulunci?

 

Insha Allahu a mako na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya don ganin amsoshin wadannan tambayoyi da kuma bukatar da Jagoran ya gabatar wa matasan.

 

------------------------------------------/

 

END

Ra'ayi