Feb 02, 2016 14:36 UTC
  • Ayatullah Sayyid Ali Khamenei
    Ayatullah Sayyid Ali Khamenei

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Iran A Mako da ke leko muku wasu daga cikin muhimman al’amurran da suka faru a Iran cikin mako wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi a kowane mako da fatan masu saurare suna cikin koshin lafiya.

Yau ma ga mu da wani sabon shirin, amma kafin mu je ga cikakken shirin ga wasu daga cikin kanun labaran da za ku ji.

 

Daga cikin batutuwan da suka dau hankula cikin makon har da jawaban da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi a ganawar da yayi da bangarori daban-daban na al’ummar Iran. Har ila yau kuma wani batun shi ne ci gaba da tattaunawar da Iran take yi da manyan kasashen duniya kan shirin nukiliyanta. Sai kuma ziyarar aiki da shugaban kasar Iran ya kai garin Qum inda ya zargi Amurka da gazawa a tattaunawar nukiliyan da Iran. A bangaren diplomasiyyar ma dai a cikin makon ne ministan harkokin wajen Iran ya kai ziyara kasar Iraki don tattaunawa da manyan jami’an kasar kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu da ma yankin baki daya. A bangaren tsaron kasa kuwa, babban lamarin da ya fi daukan hankula shi ne atisayen Rasulul A’azam da dakarun kare juyin juya halin Musulunci suka yi na kwanaki uku a mashigar Hormus da Tekun Fasha.

 

Wadannan watakila da ma wasunsu suna daga cikin batutuwan da za mu yi dubi kansu cikin shirin na mu na yau. Sai a biyo mu sannu a hankali.

 

------------------------------------------/

 

Masu saurare harkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin cewa A wata ganawa da ya yi da ‘yan kwamitin gudanar da bikin ranar injiniyoyi ta kasar Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi ishara da muhimmanci da kuma irin rawar da injiniyoyi matasa na Iran suka taka a lokuta daban-daban ciki kuwa har da lokacin gwagwarmayar juyin juya halin Musulunci da kuma lokacin kallafaffen yaki, inda ya ce: A lokacin kallafaffen yaki, injiniyoyinmu sun kasance wasu sojoji da suka sadaukar da rayukansu da kuma gabatar da dukkanin kwarewar da suke da ita, sannan kuma a kowace rana irin wannan kwarewar da suke da ita din sai kara fitowa take yi.

 

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana kokari da nasarori na ilimi da injiniyoyin na Iran suka samu bayan kallafaffen yaki da kuma irin mukamai da matsayin da suka rike a bangaren gudanar da kasar Iran a matsayin wani lamari mai muhimmancin gaske, inda ya kiraye su da cewa: Wajibi ne ku yi kokari a fagage daban-daban na kasa wajen tabbatar da batun nan na cewa "Lalle za mu iya" da kuma bayyanar da shi a aikace ga mutane. Haka nan kuma ku yi kokari wajen gano gibi da kuma bukatun da ake da su a kasa, don ku cike wadannan gibin da ake da su.

 

Har ila yau kuma a safiyar ranar Alhamis din da ta gabata ma an watsa jawabin da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi a ganawarsa da membobin kwamitocin ‘Kwamitin shahida bangaren tarbiyya' da ‘Kwamitin shahidan jami'oi' da kuma ‘Kwamitin shahidan masu gudanar da ayyuka na fasaha' mahalarta taron shahidan da aka gudanar a dakin taro na Milad Tower da ke birnin Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

 

A yayin wannan ganawar, Ayatullah Khamenei ya bayyana kasantuwar masana a lokacin kallafaffen yaki a matsayin wani lamari da ke nuni da ruhin ‘sadaukarwa a tafarkin Allah da kuma shahada' a tsakanin bangarori daban-daban na al'ummar Iran; haka nan kuma yayin da yake ishara da wajibcin jinjinawa shahidai da kuma hana duk wani abin da zai sanya a mance da su ko kuma rage kaifin ambatonsu, Jagoran cewa yayi: A hakikanin gaskiya tarurrukan jinjinawa shahidai wani ci gaba ne da tafiya a tafarkin jihadi da shahada. A saboda haka wajibi ne a ci gaba da karfafa ambaton shahidai da abubuwan da suka faru a cikin rayuwarsu.

 

Daga karshe dai Jagoran ya ce: Duk wata al'umma da aka karfafa al'adar sadaukarwa da shahada a cikinta, to kuwa wannan al'ummar za ta ci gaba, sannan kuma babu wani lokaci da za ta fuskanci matsalar koma baya.

 

----------------------------------/

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin a makon da ya wuce ne shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani da ‘yan tawagar majalisar ministocinsa suka kai ziyara lardin Qum don ganin irin ayyukan da ake yi a lardin da kuma ganawa da al’ummar lardin.

 

A wata ganawa da yayi da manema labarai, shugaba Ruhani yayin karin haske kan shirin nukiliyan zaman lafiya na kasar da kuma tattaunawar da ake yi da Amurka, inda ya zargi Amurkan da cewa ita ce take kafar ungulu ga ci gaban da ake fatan samua yayin tattaunawar.

 

Shugaban na Iran ya ce wajibi ne a kawo karshen dukkanin takunkumin zalunci da suka saba wa doka da aka sanya wa Iran a duk lokacin da aka kawo karshen tattaunawar da kuma cimma yarjejeniya.

 

Jawabin na shugaba Ruhani ya zo ne a daidai lokacin da tawagar Iran da ta hada da ministan harkokin wajen kasar da mataimakansa suke ci gaba da tattaunawa da Amurka da sauran manyan kasashen duniya kan shirin nukiliyanta na zaman lafiya.

 

A makon da ya wuce din ne ministan harkokin wajen Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya gana da takwararsa ta na kasar Iran John Kerry a ci gaba da tattaunawar da ake yi din don cimma yarjejeniya kafin wa’adin 1 ga watan Yulin da aka tsayar don cimma yarjejeniyar.

 

Har ila yau shi ma mataimakin ministan harkokin wajen na Iran sannan kuma daya daga cikin manyan masu tattaunawar Sayyid Abbas Araqchi ya gana da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniyar Yokiyo Amano a helkwatar hukumar don tattaunawa hanyoyin ci gaba da aiki tare tsakanin bangarorin biyu.

 

Dukkanin bangarorin biyu dai wato Iran a bangare guda da kuma kasashen kungiyar nan ta 5+1 a bangare guda suna ci gaba da kokari wajen ganin an cimma yarjejeniya kan shirin nukiliyan na Iran kafin wa’adin da aka diba.

 

---------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Idan dai masu saurare suna biye da mu a shirin mu da ya gabata sakamakon ci gaba da jan hankula da wasikar da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya aike wa matasan kasashen Turai da Arewacin Amurka a makonnin da suka gabata biyo bayan irin bakar farfagandar da ake yadawa kan addinin Musulunci a can din, inda ya kiraye su da su gudanar da bincike da kansu wajen gano hakikanin Musulunci, ya sanya a makon da ya wuce muka kawo muku wani bangare na wannan wasikar don sake tunawarta inda muka ce a yau za mu karkare da bangare na karshe na wasikar inda jagoran ya amsa wasu tambayoyi da ya gabatar wa matasan kamar yadda muka kawo a shirin da ya gabatan.

 

Bayan da jagoran ya gabatar da wasu tambayoyi da suka hada da cewa shin me ya sa yanzu aka dawo da tsohuwar siyasar sanya tsoro da kyamar Musulunci da musulmi? Me ya sa tsarin mulki na duniya a halin yanzu ya sanya tunani na Musulunci a gaba? Shin wasu abubuwa ne da suke cikin tunani da koyarwar Musulunci da har zai zamanto kafar ungulu ga tsare-tsare da siyasar manyan kasashen duniya, sannan kuma me za su samu wajen bakanta fuskar Musulunci?

 

Daga nan sai ya ci gaba da cewa:

 

A saboda haka, bukata ta ta farko ita ce ku yi tambaya da kuma binciko dalilin irin wannan gagarumin kokari na bata sunan Musulunci.

 

Bukata ta ta biyu, ita ce yayin mayar da martani ga irin wannan gagarumin bakar farfagandar bata sunan Musulunci (da ake yi), ku yi kokarin fahimtar wannan addini (Musulunci) da koyarwar ta hakika kai tsaye. Lafiyayyen hankali yana hukumta wajibcin sanin hakikanin abin da ake tsoratar da ku shi da kuma nesanta ku daga gare shi. Ni dai ba ina cewa ne lalle sai kun yarda da fahimta ta ko fahimtar wani kan Musulunci ba, sai dai abin da nake cewa shi ne kada ku bari a kange ku daga wannan hakikar wacce take da tasiri cikin duniyar yau saboda cimma wata bakar manufa. Kada ku bari cikin riya su gabatar muku da ‘yan ta'addan da suke karkashin ikonsu a matsayin wakilan Musulunci. Kamata yayi ku fahimci Musulunci daga tushensa na asali. Ku fahimci Musulunci ta hanyar Alkur'ani da rayuwar Annabin Musulunci (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa).

 

A nan ina son in tambaye ku, shin ya zuwa yanzu kun taba karanta Alkur'anin musulmi kai tsaye? Shin kun taba karantar koyarwar Annabin Musulunci (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa) da kyawawan halaye da ‘yan'adamtakarsa? Shin ya zuwa yanzu kun fahimci sakon Musulunci ta wata kafa ta daban, ba kafar watsa labarai ba? Shin kun taba tambayar kanku ya ya aka yi wannan Musuluncin, sannan bisa wasu koyarwa ya samu daman zama mafi girman al'adu da ci gaban ilimi da tunani na duniya sannan kuma ya tarbiyyantar da mafi girma da kyawun masana da masu tunani na duniya?

 

Ina kiranku da kada ku bari a yi amfani da bakar siyasa da wauta wajen katange ku daga gaskiya, da kuma kawar da yiyuwar yin alkalanci cikin adalci daga gare ku. A halin yanzu da kafafen sadarwa suka rusa ganuwar kan iyakokin kasashe, kada ku bari a kange ku cikin kirkirarrun kan iyakoki na boge. Duk da cewa babu wani mutum, a kan kansa, da zai cike wannan gibin da aka samar, amma kowane guda daga cikinku zai iya samar da gadar tunani da adalci a kan wannan gibin da aka haifar. Duk da cewa wannan kalubalen da aka kirkira tsakanin Musulunci da ku matasa wani kalubale ne mai sarkakiyar gaske, to amma hakan yana iya kirkiro sabbin tambayoyi cikin zukatanku da suke neman sanin hakika. Kokari wajen samo amsoshin wadannan tambayoyi, zai samar muku da wata dama ta gano wasu sabbin gaskiyar.

 

A saboda haka, kada ku bari wannan dama ta fahimtar gaskiyar Musulunci ta kubuce muku, don me yiyuwa ta hanyar wannan jin nauyi a jika da kuke da shi, al'ummomi masu zuwa za su rubuta tarihin irin wannan mu'amala da kasashen yammaci suka yi da Musulunci cikin sauki ba tare da wahala ba.

 

------------------------------------/

 

END

Tags

Ra'ayi