Feb 02, 2016 15:03 UTC
  • Taron Yarjejeniyar nukiliya
    Taron Yarjejeniyar nukiliya

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Iran A Mako da ke leko muku wasu daga cikin muhimman al’amurran da suka faru a Iran cikin mako wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi, da fatan masu saurare suna cikin koshin lafiya kuma za su kasance tare da mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.

Masu saurare daga cikin batutuwan da za mu yi dubi cikinsu cikin shirin na mu na yau ko har da batun yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya kan shirin nukiliyan zaman lafiya na kasar wanda shi ne ma lamarin da zai fi cin lokacin shirin na mu na yau. Har ila yau kuma daga cikin batutuwan da suka dau hankula a Iran din har da bukukuwan ranar Jamhuriyar Musulunci da ake gudanarwa a kowace shekara don tunawa da ranar da al’ummar Iran suka zabi tsarin Jamhuriyar Musulunci a matsayin tsarin da suke so ya mulke su bayan nasarar juyin juya halin Musulunci. Haka nan kuma sai batun zaman taron ‘yan majalisun kasashen duniya da aka gudanar a kasar Vietnam wanda tawagar Iran ma ta samu halarta. Har ila yau kuma a fagen diplomasiyya ma dai cikin makon Iran ta gudanar da ayyuka daban-daban da nufin magance matsalolin da suka kunno kai a yankin nan musamman a kasar Yeman.

 

Wadannan watakila da ma wasunsu suna daga cikin batutuwan da za mu yi dubi cikinsu a shirin na mu na yau. Don haka sai a biyo mu sannu a hankali.

 

--------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin a ranar Alhamis din makon da ya wuce ne, bayan tattaunawa ba dare ba rana ta kwanaki 9 a birnin Lausanne na kasar Switzerland, Iran da manyan kasashen duniya nan a kasashen kungiyar 5+1 suka cimma wata matsaya ta aiki tare wacce a bisa ita ce za a rubuta yarjejeniyar karshe a tsakaninsu kan shirin nukiliyan zaman lfiya na kasar Iran.

 

Jim kadan bayan cimma yarjejeniyar, ministan harkokin wajen Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif wanda ke jagorantar tawagar Iran da kuma takwararsa ta Tarayyar Turai Federica Mogherini a madadin manyan kasashen duniya suka sanar da cimma yarjejeniya da kuma karanto matanin abin da aka cimma din.

 

Yazo cikin sanarwar cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasashen kungiyar 5+1 da suka kumshin Amurka, China, Rasha, Faransa, Birtaniyya da Jamus, bayan tattaunawa na tsawon lokaci sun cimma yarjejeniya ta hadin gwiwa da kuma aiki tare karkashin tsarin abin da aka cimma tsakanin bangarorin biyu a ranar 24 ga watan Nuwamban 2013.

 

A bisa yarjejeniyar dai dukkanin cibiyoyin nukiliyan Iran da suka hada da na Natanz, Fordo, Esfahan da Arak duk za su ci gaba da ayyukansu babu guda da za a rufe shi, sai dai kawai sauyin aikin wajen. Haka nan kuma Iran za ta ci gaba da tace sinadarin uranium din da take da shi a cikin gida. Don haka Iran za ta ci gaba da samar da makamashin da take bukata a fagen shirin nukiliyanta na zaman lafiya da kanta da kanta. Har ila yau kuma an cimma yarjejeniyar cewa wannan tsari na aiki tare da aka cimma da kuma sanya hannu kansa zai kasance na tsawon shekaru 10. Tsawon wannan lokacin Iran za ta ci gaba da amfani da bututun tace sinadarin uranium (da aka fi sani da centrifuge) guda 5000 a cibiyar nukiliyanta da ke garin Natanz wadanda za su ci gaba da tace sinadarin uranium har zuwa kashi 3.67. Ita kuwa cibiyar nukiliya da ke Fordo, za a mayar da ita wata cibiya ce ta gudanar da bincike na nukiliya maimakon tace sinadarin uranium. Za a ci gaba da kiyaye bututun tace sinadarin uranium sama da 1000 da suke Fordo din da kuma ci gaba da kiyaye su. Haka nan kuma za a mayar da rabin kayayyakin aikin cibiyar ta Fordo, bisa taimakon wasu kasashen waje, su zamanto wani waje na gudanar da binciken da ya shafin nukiliyan.

 

To dangane da cibiyar nukiliyan na Iran da ke garin Arak kuwa, bangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar cewa za a ci gaba da kiyaye shi da kuma aikin da ya ke yi sai dai kuma za a ma kara karfafa shi da mai she shi na zamani. Kamar yadda kuma Iran za ta ci gaba da ba da hadin kai ga hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya don ci gaba da gudanar da bincike da kuma sanya ido kan shirin nukiliyan na Iran.

 

To wannan bangaren nauyin da ya hau kan Iran kenan.

 

To a bangare guda kuma, a bisa yarjejeniayr da aka cimma din, su ma kasashen duniyan suna da wani nauyi a wuyansu.

 

Na farko dai bayan aiwatar da abin da aka cimma din, za a dage wa Iran dukkanin takunkuin da kwamitin tsaron MDD ya sanya mata. Na biyu za a dauke wa Iran takunkumin da wasu kasashen Turai suka sanya mata, haka nan da wadanda Amurka ma ta sanya mata ciki kuwa har da takunkumi na kudi, ayyukan bankuna, inshora zuba hannun jari da dukkanin lamurran da suke da alaka da hakan a bangarori daban-daban da suka hada da bangaren man fetur, iskar gas, danjin man fetur da kera motoci. Na uku har ila yau kuma za a dage duk wani takunkumin da aka sanya wa wasu mutanen Iran da suka hada da jami’an gwamanti da na masu zaman kansu, haka nan kuma da cibiyoyin da suka da alaka da gwamnatin Iran ko kuma na ‘yan kasuwa da suka hada da babban bankin kasar da sauran bankuna da cibiyoyin kudi, kamfanonin sufuri na ruwa da na sama na Iran da jiragen jigilan man fetur da dai sauransu.

 

-------------------------------------------/

 

Wannan a takaice shi ne abin da yarjejeniyar ta kumsa.

 

Tun dai bayan sanar da wannan labarin cimma yarjejeniyar jami’ai da al’ummar Iran suka yi na’am da kuma nuna farin cikinsu da ita, a daidai lokacin da wasu irin su HKI da wasu kasashen larabawa irin su Saudiyya suke ci gaba da nuna rashin jin dadinsu kan haka, lamarin da wasu suke gani a matsayin wata alama da ke tatabbatar da cewa al’ummar Iran da kuma gwamnatin aksar ce ta suka yi nasara a yayin wannan yarjejeniyar.

 

Dubi cikin lamarin kuwa da idon basira zai iya tabbatar da hakan a fili. Don kuwa na farko dai babu wani guda daga cikin cibiyoyin nukiliyan Iran da aka rufe shi gaba daya kamar yadda tun farko wasu kasashen musamman Amurkawa da na Turai suka so ba. Na biyu Iran za ta ci gaba da tace sinadarin uranium din da take bukata a cikin gida ba kamar yadda wasu suka so hana ta wannan hakkin ba. Na uku kasashen duniya sun amince da hakkin da Iran take da shin a mallakar fasahar nukiliya sabanin yadda a da suka tsaya kyam da kuma kokari wajen ganin sun hana ta wannan hakkin. Na’am gaskiya ce cewa an takaita wasu ayyukan na nukiliyan na Iran ko kuma kamar yadda wasunsu suke fadi wai an hana Iran mallakar makamin nukiliya, don haka suke ganin abin da aka cimma din a matsayin wata nasara a gare su. To amma wace nasara. Tun farko dai Iran ba ta taba wani yunkuri na kera makamin nukiliya ba, su kan su turawan sun san da haka. Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei har fatawa ya fitar na haramcin kera irin wadannan makaman, lamarin da shugaban Amurka ya sha fadin hakan a fili. Don haka ai da man babu wata magana makamancin hakan. Har ila yau kuma ga batun dage takunkumin zaluncin da aka sanya wa kasar na tsawon shekaru ba bisa da doka ba.

 

---------------------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Ranar larabar makon da ya wuce ne, wato 12 ga watan Farvardin ta yi daidai da ranar Jamhuriyar Musulunci a nan kasar Iran inda ake gudanar da bukukuwa daban-daban don murnar wannan ranar a duk fadin kasar; ranar da ake ganinta a matsayin wata alama ta nuna kaunar al’ummar Iran ga tsarin Musulunci na kasar da kuma tabbatar da shi.

 

Ko shakka babu ranar 12 ga watan Farvardin tana da cikin ranaku masu muhimmancin gaske ga kasar Iran da kuma juyin juya halin Musulunci na kasar. Saboda a wannan ranar ce, wato 12 ga watan Farvardin na shekarar 1358 wato 1 ga watan Aprilun 1979 rana ce da al’ummar Iran suka fito kwansu da kwarkwatansu don kada kuri’arsu a zaben jin ra’ayin al’umma da marigayi Imam Khumaini (r.a) ya bukata a yi don ba wa mutane damar su zabin tsarin da suke so ya mulke su, duk kuwa da cewa wata da watanni ne kenan da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar. Imam yana iya tilastawa mutane tsarin Musulunci a kansu. Don kuwa tun farko ma shi ne tushen gwagwarmaya da kuma juyin juya halin Musulunci da ya jagoranta; wato manufar juyin ita ce kafa tsari irin na Musulunci. To amma duk da haka Imam ya ce a gabatar wa mutane wannan tsarin a ji ra’ayinsu shin sun amince da shi ko a’a.

 

Alhamdu lillahi bayan kada kuri’ar, sakamako ya nuna cewa kashi 90 da wani abu cikin dari na mutanen kasar sun amince da wannan tsari ne na Musulunci ya mulke su. don haka wannan ranar ta zamanto wata rana mai muhimmanci ga al’ummar Iran da kuma jagororin kasar don kuwa wata ran ace kana kuma wata alama ce da take nuni da sabon salon tsarin demokradiyya wanda Musulunci ya gabatar da shi.

 

Irin wannan so da kaunar da marigayi Imam Khumaini (r.a) sannan kuma a bayansa Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Khamenei yake nuna wa mutane da kuma share musu fagen fadin albarkacin bakinsu da kuma girmama dukkanin abubuwan da suke so, hakan ne ya sanya wannan tsari na Musulunci har ya zuwa yanzu bayan shekaru sama da 36 da kafuwarsa amma har yanzu yana nan daram kuma jama’a suna ci gaba da goyon bayansa da kuma sadaukar da komai saboda shi; duk kuwa da matsalolin da makiya suka sanya al’umma da kuma tsarin ciki tsawon wadannan shekaru 36 da wani abin.

 

-------------------------------------------/

 

END

Tags

Ra'ayi