Feb 29, 2016 09:11 UTC
  • Dambarwar Siyasa A Burundi
    Dambarwar Siyasa A Burundi

Jama’a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wanann shiri na Afirka a mako.

Shirin kan yi a dubi a kan muhimman lamurra da suka wakana a nahiyar Afirka a cikin mako, a yau kamar kowane mako da yardar Allah za mu duba wasu daga cikin muhimman lamaurra da suka wakana a wannan mako a nahiyar, daga ciki kuwa har da batun safkar ruwan sama kamar da bakin kwarya a jamhuriyar, da kuma batutuwan tsaro da siyasa a Najeriya da kuma Burundi, da ma wasu kasashen gwargwadon yadda lokaci ya bamu hali, da fatan za a kasance tare da mu a cikin shirin.

……………………………..

To bari mu fara da batun ambaliyar ruwan sama a J. Nijar, inda a cikin wannan mako ne ofishin majalisar dinkin duniya mai kula da ayyukan jin kai ya sanar da cewa akalla mutane 4 sun rasa rayukansu wasu dubbai kuma sun rasa gidajensu a yankuna daban-daban na Jamhuriyar Nijar, sakamakon safkar ruwan sama kamar da baki kwarya a yankuna da dama na kasar.

A nasu bangaren mahukunta a Yamai babban birnin jamhuriyar ta Nijar sun bukaci mazauna yankunan da ke kusa da teku da su gaggauta tashi, domin guje wa ambaliyar ruwa da ka iya faruwa, sakamakon cikar da tekun ya yi taf da ruwa.

…………………………….

To a can tarayyar Najeriya ma hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA ta sanar da cewa akwai yiwuwar a iya samun ambaliyar ruwa a wasu yankuna da ke kusa da kogin Benue, bayan samun sanarwa daga mahukuntan Kamaru da ke cewa za a bude wani babban dam na kasar domin rage ruwan da ke cikinsa bayan ya cika ya bashe. Hakan ne ya sanya hukumar shirya tarukan wayar da kan jama’a a wasu yankuna na kasar

……………………………….

To har yanzu a tarayyar ta Najeriya shugaban kasar Muhammad Buhari na ci gaba da jadda matsayin na ganin cewa an dawo da biliyoyin dalolin kasar da aka sace a kai kasashen ketare, wanda hakan ya sanya masana da dama suke ta bayyana’a ra’ayoyinsu kan wannan batu, kuma da dama daga cikinsu na goyon bayan wannan mataki na shugaba Buhari.

……………………………….

To a bangaren siyasa kuwa, matasa masu goyon bayan shugaba Janar Buhari ne suka ja kunnen ‘yan majalisar dokokin Najeriya kan su mayar da hankali ga abin da jama’a suka zabe shi saboda shi, tare da yin barazanar daukar matakai a kan duk wani dan majalisa da ke wasa aikinsa, ko da kuwa hakan zai kai ga bin kaidoji ne yin kiranye a kansa.

………………………………

A kan batun danbarwar siyasar kasar Burindi kuwa, kungiyar tarayyar Afirka ta bayyana cewa akwai hadari dangane da yanayin da ake ciki a kasar, wand aka iya kai kasar zuwa ga yakin basasa.

Tarayyar Afirka ta kirayi dukkanin bangarorin da ba su ga maciji da juna a kasar da suka hada da bangaren gwamnati da kuma sauran jam’iyyun adawa da su warware matsalolinsu ta hanyar lumana.

A kwanakin baya ne aka kasashe bababn kwamnadan sojojin kasar a birnin Bujumbura, haka nan kuma an kashe jigajigan jam’iyyuna adawa da dama  acikin ‘yan lokutan nan a kasar.

Music……………………….

To jama’a lokacin da muke da shi ya kawo jiki a nan za mu dasa aya sai a mako na gaba za a ji mu dauke da wani shirin da yardarm Allah, kafin lokacin a madadin wadanda suka hada sautin shirina  faifai ha ya kammala, nake yi muku fatan alkhairi wassalamu alaikum wa rahmatullah.

 

 

 

Tags

Ra'ayi