Feb 02, 2016 15:05 UTC
  • Imam Khamenei
    Imam Khamenei

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Iran A Mako da ke leko muku wasu daga cikin muhimman al’amurran da suka faru a Iran cikin mako wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi, da fatan kuna cikin koshin lafiya kuma za ku kasance tare da mu tun daga farkon shirin har zuwa karshensa.

Kamar yadda muka saba ga wasu daga cikin kanun labaran abubuwan da za mu leko muku a cikin shirin na mu na yau. Daga cikin su akwai bukukuwa maulidin haihuwar Imam Ali (a.s) da aka gudanar a duk fadin Iran. Haka nan kuma a cikin makon ne Jagoran juyin juya halin Musulunci ya gana da dubun dubatan ma’aikatan Iran da suka kai masa ziyara a daidai lokacin da ake gudanar da ranar ma’aikata ta duniya. Haka nan kuma a cikin makon ne dai aka sake zama teburin tattaunawa tsakanin Iran da manyan kasashen duniya kan shirin nukiliyanta na zaman lafiya. Haka nan kuma a cikin makon ne dai ministan tsaron kasar Siriya ya kawo ziyara nan Iran a bisa gayyatar takwararsa na Iran. Haka nan a bangaren kasa da kasa ma din dai a cikin makon kungiyar agaji ta Red Crescent ta Iran ta ci gaba da kokarinta na isar da kayayyakin taimakon gaggawa da al’ummomin da suke bukata musamman a kasashen Yemen da Iraki da Siriya da sauransu.

 

Wadannan watakila da ma wasunsu suna daga cikin batutuwan da za mu yi dubi cikin su a sirin na mu na yau. Sai a biyo mu sannu a hankali.

 

-----------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda watakila kika ji a farkon shirin a farkon makon ne wanda yayi daidai da ranar haihuwar Amirul Muminin (a.s), Imamin farko daga cikin Imaman Ahlulbaiti (a.s) aka gudanar da bukukuwan murna a duk fadin kasar Iran inda al’ummar musulmin kasar suka biyo sahun sauran ‘yan’uwansu musamman mabiya tafarkin Ahlulbaiti (a.s) na duniya wajen gudanar da wannan bikin. Har ila yau kuma a ranar asabar din ce dai ta yi daidai da zagayowar ranar shahadar Ayatullah Shahid Murtadha Mutahari, ranar da aka ba ta sunan ranar Malamai inda a nan ma aka gudanar da bukukuwa tunawa da wannan ranar da kuma irin gagarumar rawar da Ayatullah Mutaharin ya bayar a fagen ilimi inda aka karrama wasu daga cikin malaman da su ma suka taka gagarumar rawa a wannan fagen.

 

Da hakan ne za mu fara shirin na mu na yau.

 

A karshen makon da ya wuce ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubun dubatan ma'aikatan kasar Iran da suka fito daga bangarori daban-daban na kasar don jinjinawa irin tsayin daka da kuma nuna sanin ya kamata da ma'aikatan Iran suka nuna tsawon shekaru talatin din da suka gabata a gaban makirce-makirce da matsin lamba na ciki da wajen kasar, inda ya ce: A hakikanin gaskiya ma'aikata sun taka gagarumar rawa wajen kokari da kuma ciyar da kasar nan gaba ta hanyar hakuri da kuma jurewa matsaloli da wahalhalu. A saboda haka wajibi ne jami'an gwamnati su girmama da kuma jinjinawa wannan kokari da sadaukarwa ta hanyar kara kaimi wajen magance matsalolin da ma'aikatan suke fuskanta.

 

Haka nan kuma a ci gaba da bayanyin nauyin da ke wuyan jami’an gwamnati da cibiyoyi daban-daban na gwamnatin da suke da alaka da samar da kayayyakin da ake bukata a cikin gida, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa yayi: Mabudin magance matsalolin tattalin arzikin (da Iran take fuskanta) ba a Lausanne ko Geneva ko New York yake ba,face dai a cikin gida yake. A saboda haka wajibi ne kowa yayi kokarin sauke nauyin da ke wuyansa wajen karfafa abubuwan da ake samarwa a cikin gida a matsayin hanya guda daya tilo ta magance matsalar tattalin arziki.

 

Jagoran ya ce tabbas takunkumin zaluncin da aka sanya wa Iran ya haifar da wasu matsalolin, to amma ko shakka babu takunkumi da matsin lamba ba za su iya hana yunkuri na al'umma da kuma tsare-tsaren da ake da su wajen ciyar da harkar samar da kayyakin da ake samarwa a cikin gida ba gaba ba. Don haka ne ma Ayatullah Khamenei yayi ishara da gagarumar nasarar da Iran ta samu a fagen soji, kera madatsan ruwa, fasahar Nano, fasahar nukiliya da dai sauransu, a matsayin abubuwan da ke tabbatar da cewa takunkumin ya gaza wajen hana al’ummar Iran ci gaba.

 

--------------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin a ranar Larabar makon da ya wuce ne jami’an Iran da na manyan kasashen duniya da suke tattaunawa da Iran kan shirin nukiliyanta na zaman lafiya suka sake komawa kan teburin tattaunawa da nufin tsara yadda yarjejeniyar karshe tsakanin bangarori biyu za ta kasance kan shirin nukiliyan zaman lafiyan na Iran.

 

Zaman dai ta kasance ne tsakanin jami’an na Iran karkashin jagorancin mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sayyid Abbas Araqchi da takwaransa na tarayyar Turai.

 

Rahotanni sun ce babban lamarin da aka fara tattaunawar shi ne batun cire wa Iran takunkumin da aka sanya mata kan shirin nukiliyan nata da kuma yadda za a cire su din.

 

Jami’an kasar Iran dai sun bayyana cewar ya zuwa yanzu dai sun tabbatar da kyakkyawar aniyar da suke da ita, don haka fata da kuma abin da suke fatan gani shi ne irin wannan yanayin daga wajen daya bangaren da suke tattaunawa din da kuma cika alkawarin da suka dauka a tattaunawar da aka gudanar a baya da kuma nauyin da suka hau kansu.

 

Ya zuwa yanzu Iran ta cika alkawurra da kuma nauyin dake wuyanta kamar yadda hatta cibiyoyin da suke sanya ido kan wannan lamarin sun tabbatar da hakan, don haka babban abin da take so shi ne bangaren manyan kasashen duniya su ma su yi haka ciki kuwa har da dage wa Iran dukkanin takunkumin da aka sanya mata ta hanyar fakewa da wannan batu na nukiliyan.

 

Tsawon wadannan lokuta, hatta a kwanakin baya-bayan nan jami’an Iran sun tabbatar da aniyarsu da kuma cewa akwai yiyuwar a cimma yarjejeniyar matukar dai manyan kasashen duniyan suka girmama abin da aka cimma da kuma nesantar mika kai ga matsin lambar da sahyoniyawan duniya suke yi musu, lamarin da ya sanya a kwanakin shugaban majalisar shawarar Musulunci ta Iran Dakta Ali Larijanin yin barazanar cewa matukar bangaren da ake tattaunawa da shi din ya ki cika alkawari da kuma nauyin da ke wuyansa, to Iran za ta ci gaba da tace sinadarin uranium din da take yi daidai da yadda take so.

 

----------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin a cikin makon, jami’an kasashe daban-daban na duniya sun kawo ziyara nan Iran a kokarin karfafa alakar da ke tsakaninsu da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

 

A cikin makon ne dai ministan tsaron kasar Siriya Janar Fahd Jasim Freigh ya kawo ziyarar aiki nan Iran inda ya gana da takwararsa na Iran Birgediya Janar Husain Dehghan, shugaban majalisar Ali Larijani da kuma babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Admiral Ali Shamkani inda suka tattauna kan yanayin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya, fada da ta’addanci da sauran batutuwan da suka shafi kasashen biyu.

 

A ganawar da yayi da manema labarai jim kadan bayan ganawa da ministan tsaron kasar Siriyan, ministan tsaron Iran Janar Dehghan ya bayyana yakin da ke faruwa a kasar Siriya a matsayin wani yaki na wakilci don biyan bukatar HKI da Amurka inda yace: manufar wannan yaki ita ce tabbatar da tsaron HKI, raunanawa da kuma rarraba kasashen musulmi, sauya taswirar Gabas ta tsakiya bugu da kari kan fada da gagarumar farkawa ta Musulunci da ta mamaye yankin.

 

Don haka ministan tsaron na Iran ya bayyana samar da wani karfi na hadin gwiwa da nufin fada da wannan annoba ta ta’addanci da ta addabin yankin Gabas ta tsakiyan a matsayin wani wajibi na hakika. Don haka ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da kasancewa tare da al’ummar Siriya da hukumar kasar wajen cimma wannan manufa ta tumbuke tushen ta’addancin.

 

Shi ma a nasa bangaren, shugaban majalisar shawarar Musulunci ta Iran Dakta Ali Larijani, a wata ganawa da yayi da ministan tsaron na Siriya ya bayyana aniyar Iran na ci gaba da kyautata alaka da kasar Siriya kamar yadda kuma suka tattauna kan batutuwa daban-daban da suka shafi bangarorin biyu.

 

Shi ma babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar ta Iran Admiral Shamkhani, a ganawar da yayi da ministan tsaron na Siriya, ya bayyana irin matsayi mai girma da Siriya take da shi inda ya ce a halin yanzu ya bayyana cewar babu abin da rikici da yake-yake zai kai duniya in ban da karin dagula lamurra don haka hanya guda kawai ta magance matsalolin da suka kunno kai ita ce tattaunawa da hanyoyin na diplomasiyya.

 

-----------------------------------------/

 

Sakamakon ci gaba da kai hare-haren wuce gona da irin da Saudiyya take yi a kan al’ummar Yemen bugu da kari kan hare-haren ta’addancin da ‘yan ta’addan da suke samun goyon bayan kasashen larabawa irin su Saudiyya din suke ci gaba da kai wa kasashen Siriya da Iraki da sauran, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sake sanar da shirinta na aikewa da kayayyakin agaji don ceto miliyoyin al’ummomin wadannan kasashen musamman na kasar Yemen da suke cikin mawuyacin hali.

 

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran din kan harkokin kasashen Afirka da na larabawa Husein Amir Abdullahiyan ne ya bayyana hakan a wata ganawa da yayi da babban jami’in kungiyar agaji ta Red Cross a yankin Gabas ta tsakiya wanda ya kawo ziyarar aiki na Iran.

 

Cikin ‘yan kwanakin nan dai Iran sha kokarin aikewa da jiragenta dauke da kayayyakin agaji zuwa ga al’ummar Yemen din sai dai kuma jiragen yakin Saudiyya sun hana isar wadannan jiragen sakamakon ci gaba da kai hare-haren da suke kai wa filayen jiragen saman Yemen din.

 

Hakan ne ma ya sanya kakakin Ma’aikatar harkokin wajen Iran Malama Mardhiyeh Afkham ta bayyana cewar ci gaba da killacewa al’ummar Yemen wani lamari ne da ya saba wa dan’adamtaka sannan kuma matakin da gwamnatin Saudiyya ta dauka na hana isar wa mutanen Yemen din da kayayyakin agaji na gaggawa da suke bukata wani lamari ne da ke ci gaba da jefa al’ummar kasar cikin mawuyacin hali.

 

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ta kara da cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gama dukkanin shirin aikewa da kayayyakin agaji na gaggawa ga al’ummar Yemen sai dai kuma gwamnatin Saudiyya ce take hana hakan, tana mai cewa Iran za ta ci gaba da bin hanyoyin da suke dace ta hanyar kungiyar Red Cross ta duniya wajen ganin an saukaka wa mutanen Yemen din wannan mawuyacin hali da suke ciki.

 

Har ila yau Malama Afkham ta yi kakkausar suka ga yadda sojojin Saudiyya suke amfani da makaman da aka haramta a duniya a kan al’ummar Yemen din alhali mayan kasashen duniaya sun yi shiru suna ci gaba da zuba ido, kai wasu ma da hannunsu cikin hakan.

Tags

Ra'ayi