Feb 02, 2016 15:06 UTC
  • Taron hadin kan al\'ummar Musulmi a kasar Iran
    Taron hadin kan al\'ummar Musulmi a kasar Iran

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Iran A Mako da ke leko muku wasu daga cikin muhimman al’amurran da suka faru a Iran cikin mako wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi a kowane mako da fatan masu saurare suna cikin koshin lafiya.

Kamar yadda muka saba ga wasu daga cikin muhimman al’amurran da suka farun kana mu yi karin haske kansu.

 

Daga cikin batutuwan da suka dau hankula a Iran cikin makon har da bukukuwan makon hadin kai don tunawa da ranakun haihuwar Fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu (s.a.w.a) da kuma bukukuwan tunawa da ranar haihuwar Annabi Isa (a.s) da mabiya addinin Kirista na kasar suke gudanarwa, haka nan kuma da batun fara rajistar ‘yan takarar zabubbukan majalisun kwararru ta jagoranci da kuma ta shawarar Musulunci da za a gudanar a watanni masu zuwa. Har ila yau kuma jami’an diplomasiyyar Iran sun yi karin haske dangane da yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya biyo bayan da kokarin kafar ungulun da wasu ‘yan majalisar Amurka suke kokarin yi wa hakan, baya ga ziyarar aiki da wasu jami’an kasashe daban-daban na duniya da suka kawo nan Iran.

 

Wadannan suna daga cikin batutuwan da za mu yi dubi cikinsu a shirin na mu na yau, sai a biyo mu sannu a hankali.

 

--------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin a ranar Alhamis din da ta gabata, wacce ta yi daidai da ranar 12 ga watan Rabiul Awwal aka fara gudanar da bukukuwan Makon Hadin Kai a duk fadin kasar Iran da wasu kasashen Musulmi na duniya don tunawa da ranakun da aka haifi Ma’aikin Allah Muhammad (s.a.w.a).

 

A bisa riwayoyin da mabiya tafarkin Ahlul Sunna suka yi amanna da su an haifi Fiyayyen halitta (s.a.w.a) ne a ranar 12 ga watan Rabiul Awwal, kana su kuma mabiyar tafarkin Shi’a sun yi amanna da cewa haihuwar tasa ta kasance ne a ranar 17 ga watan Rabi’ul Awwal, hakan ne ya sanya marigayi Imam Khumaini, wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya ayyana ranaku biyar din da suke tsakanin wadannan ranaku biyu a matsayin ranakun Makon Hadin Kai a tsakanin al’ummar Musulmi na duniya.

 

A nan Iran dai akan gudanar da tarurruka daban-daban na kasa da kasa kan hadin kan al’ummar musulmi inda mahalarta taron daga kasashe daban-daban na duniya suke tattaunawa da musayen ra’ayi kan hanyoyi daban-daban da za a bi wajen tabbatar da hadin kai tsakanin musulmi da kuma magance matsaloli daban daban da suke addabarsu.

 

Har ila yau kuma kamar yadda muka ce ranar Juma’ar da ta gabata, wacce ta yi daidai da ranar 25 ga watan Disamba, wato ranar da mafi yawa daga cikin mabiya addinin Kirista suka yi amanna da cewa ita ce ranar haihuwar Annabi Isa (a.s), mabiya addinin Kirista a Iran suka gudanar da bukukuwan ranar Kirsimetin.

 

A irin wadannan ranakun, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kai ziyara zuwa gidajen wasu daga cikin Kiristocin Iran da suka rasa rayukansu yayin kallafaffen yakin da tsohuwar gwamnatin Iraki ta kallafawa Iran don jinjina wa iyalansu da kuma taya su murnar Kirsimetin.

 

Muna taya al’ummar Musulmi da kuma kiristocin duniya murnar wadannan ranaku masu albarka.

 

---------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin, cikin kwanakin nan an fara shirye-shiryen gudanar da zabubbukan majalisu biyu masu muhimmanci a Iran, wato zaben ‘yan majalisar kwararru ta jagoranci da kuma majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran.

 

A wata ganawa da yayi da manema labarai, ministan cikin gidan Iran, Abdurridha Rahmani Fadhli, wanda ma’aikatarsa take da alhakin gudanar da wadannan zabubbukan, ya bayyana cewar an gama dukkanin shirye-shirye, bisa hadin gwiwan majalisar kiyaye tsarin mulki, wacce take da hakkin sanya ido kan zaben da kuma amincewa da ‘yan takarar.

 

A ranar Juma’ar da ta gabata ce aka kawo karshen rajistar ‘yan takaran wadannan zabubbuka guda biyu. Ministan cikin gidan na Iran ya bayyana cewar an samu karuwar ‘yan takara da kashi 62 cikin dari na ‘yan takarar zaben ‘yan majalisar kwararrun sannan da kashi 61 cikin dari na ‘yan takaran zaben ‘yan majalisar shawarar Musuluncin idan aka kwatanta da zaben karshe na wadannan majalisu da aka gudanar a shekarun baya.

 

Kamar yadda aka tsara za a ci gaba tantance ‘yan takarar da suka yi rajistar sunansu don tsayawa takarar zama ‘yan majalisar shawarar Musulunci har zuwa ranar 4 ga watan Janairun shekara mai zuwa, sannan daga karshe kuma a ranar 9 ga watan Fabrairun shekara ta 2016 majalisar kula da kundin tsarin mulkin za su gabatar da sunaye na karshe na ‘yan takarar ga ma’aikatar cikin gidan don gabatar da su da kuma fara mataki na gaba da suka hada da yakin neman zabe da sauransu.

 

Ita dai majalisar kwararru ta jagorancin, kamar yadda doka ta 107 ta kundin tsarin mulkin Iran ta tanadar, ita ce majalisar da take da alhakin zaba da kuma sanya ido kan ayyukan Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar ta Iran, hakan ne ya sanya majalisar ta kasance daya daga cikin majalisu masu muhimmanci a kasar saboda irin matsayin da Jagoran yake da shi a tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Kamar yadda ita kuma majalisar shawarar Musulunci ita ce take da alhakin kafa dokoki a kasar.

 

--------------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

A daidai ci gaba da bayani da kuma shirye-shiryen fara aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya dangane da shirin nukiliyanta na zaman lafiya, mataimakin ministan harkokin waje na kasar Iran kuma daya daga cikin manyan jami’an Iran masu tattaunawa kan wannan batun Sayyid Abbas Araqchi ya bayyana cewar kafa dokar takaita ba wa Iraniyawa visar shiga kasar Amurka da wasu ‘yan majalisar kasar suke gabatarwa ta saba wa yarjejeniyar aiki tare da aka cimma tsakanin bangarorin biyu.

 

Mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya kara da cewa kafa wannan dokar zai yi tasiri a fagen tattalin arziki, yawon shakatawa da ilimi da al’adu, wanda a mahangar Jamhuriyar Musulunci ta Iran hakan yin karen tsaye ne ga yarjejeniyar da aka cimma.

 

Sayyid Araqchi ya ci gaba da cewa matukar Amurka ta aiwatar da wannan doka, to kuwa Iran za ta rubuta wa kwamitin da ke da alhakin sanya ido kan aiwatar da yarjejeniyar.

 

A bisa wannan doka ta majalisar dokokin Amurkan, kowane mutum daga cikin ‘yan kasashe 38 da suke cikin kasashen da Amurka ta yarda da ta soke batun wajibcin neman takardar izinin shiga Amurka a gare su, to amma daga yanzu duk wani daga cikin ‘yan wadannan kasashen da bisa kowane irin dalili ne ya tafi kasashen Iran, Iraki, Siriya ko Sudan cikin shekaru biyar din da suka gabata ko kuma a nan gaba zai tafi, to wajibi ne ya nemi visa idan yana son shiga Amurkan. Wanda hakan zai sanya ‘yan kasuwa da masu yawon shakatawa da sauransu da suke son zuwa Iran su sake ra’ayi wanda hakan yana iya cutar da bangaren tattalin arziki da yawon shakatawa hatta ma ilimi da al’adu.

 

-----------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

To har yanzu a bangaren diplomasiyya da alakokin kasashe, kasashen Iran da Aljeriya sun sanar da aniyar da suke da ita wajen dukufa wajen ganin sun bunkasa harkokin tattalin arziki da cinikayya a dukkanin bangarori a tsakaninsu.

Jakadan kasar Iran a kasar Aljeriya Rida Amiri ne ya fadi hakan a birnin Algiers, babban birnin kasar Aljeriyan inda yace an fara aiwatar da yarjeniyoyin da aka sanya wa hannu a tsakanin Iran da Aljeriya a ziyarar da mataimakin shugaban kasar Iran Ishaaq Jahngiri ya kai a kasar ta Aljeriya a kwanakin baya.

 

Amiri ya ce kasar Aljeriya na daga cikin kasashen da suka tsaya kai da fata wajen yin mu'amala da kasarsa a karkashin takunkumin da kasashen turai suka saka mata na tsawon shekaru, a kan haka ya ce a halin yanzu kasar Aljeriya na daya daga cikin kasashe da za su zama a sahun gaba wajen hulda ta cinikayya tsakaninta da Iran a dukkanin bangarori.

 

A lokuta da dama Iran ta sha sanar da cewa babbar siyasarta ita ce karfafa alaka da kasashen makwabta da kuma na musulmi don amfanuwar dukkanin bangarorin biyu.

 

----------------------------/

 

END

Tags

Ra'ayi