Mar 12, 2017 05:43 UTC

Shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,

Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, AShirin da ya gabata mun yi bayyani kan dabi'ar gaggauta tuba ga Allah madaukakin sarki, a shirin na yau kuma za mu yi bayyani kan dabi'ar gaggauta neman Tuba da kuma dawwama a kan neman gafara watau Istigafari ga Allah madaukakin sarki, amma kafin shiga cikin Shirin ga Wannan.

**********************Musuc************************

Masu Saurare, Hakika Dabi'antuwa da dabi'ar gaggauta Tuba da kuma dawwama a kan neman gafarar Ubangiji nada albarka mai yawa, daga ciki kuwa har da Karin arziki  na dukkanin misdakinsa, madiya ne ko ma'anawiya ne watau arzikin da Mutum zai samu na zahiri a wannan Duniya ne ko kuma wadatar zuci ce da kuma wacce Bawa zai riska a ranar Alkiyama, wannan shi ne Alkur'ani mai girma ya yi ishara da shi cikin Kissar Annabi Nuhu (a.s) a yayi da yake bayyani ga Mutanan sa yana mai cewa:(Sannan na ce:" Ku nemi gafarar Ubangijinku, Hakika Shi Ya Kasance mai gafara ne*Zai saukar muku Sama ta kwararo muku da ruwa*kuma ya da dade ku da dukiyoyi da 'ya'yaye, ya kuma sanya muku gonaki ya kuma gudanar muku koramu) suratu Nuhu daga Aya ta 10 zuwa ta 12.kamar yadda cikin Suratu Hudu Allah tabarka wa ta'ala ya Ambato hikayar Annabi Hudu  (a.s) da ya kasance Annabi mai hakuri yayin da yake yiwa Mutanansa Khuduba yana mai cewa:(Kuma Yak u Mutanena, ku nemi gafarar Ubangijinku sannan ku tuba gare shi, zai saukar muku da makadin (ruwhin) sama, zai kuma kara muku karfi a kan karfinku, kada kuma ku ba da baya kuna masu aikata Laifi) suratu Hudu Aya ta 52.abin fahimta a cikin wadannan Ayoyi na Alkur'ani mai girma shi ne daga cikin albarkar dabi'antuwa da dabi'ar gaggautawa da kuma dawwama a kan Istigfari da neman gafarar Ubagiji, shi ne hanya ta Karin karfin Mutum, alhali a yayin cewa rashin dabi'antuwa da wannan dabi'a yana kai Mutum ya kasance cikin Mujrimai masu laifi, da fatan Allah ya kiyaye mu da irin wadannan aiyuka da dabi'u.Masu Saurare, dabi'antuwa kuma da dabi'ar gaggautawa da kuma dawwama a kan Istigfari na daga cikin Misdakin dabi'antuwa da dabi'ar zababbun bayi da kuma shiga cikin sahunsu,Su ne masoyan Allah madaukakin sarki, Na'am cikin Littafin Alwasa'il, an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce:(an tambayi Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka a kan zababbun bayi, sai ya ce: su ne wadanda idan suka kyautata za su yi farin ciki, idan kuma suka yi laifi, za su nemi gafara, idan kuma aka basu za su yi godiya, idan kuma aka jarabce su da wani abu, za su yi hakuri, idan kuma aka bata musu rai za su yafe). Har ila yau daga cikin albarkar dake tattare da wannan dabi'a mai albarka, yafewa da kuma shafe zunubai na wanda Mutum ya sani da ma wanda bai sani ba. Kamar yadda Hadisin Annabin Rahama tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidanan tsarkaka ya yi ishara:(Ko wani abu yanada magani, maganin zunubi kuma shi ne Istigfari ko kuma neman gafara), Masu Saurare, Hakika dabi'antuwa da dabi'ar gaggauta zuwa ga neman gafarar Ubangiji, na daga cikin hanyoyin samun rahamar Ubangiji na samun tsira a Lahira da kuma kankare zunuban da Mutum ya sani da ma wanda bai sani a wannan Duniya ba, a cikin Littafin Raudatul-Muttakin an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce:( Duk wanda ya aikata wani Laifi za a jinkita rubuta masa zunubi har tsahon awowi bakwai na rana, idan Bawan da ya aikata laifi ya ce Ina neman gafarar Allah da babu wani abin Bauta sai shi, Rayayya wada Rayuwarsa ba ta da karshe, tsayayye da kansa wand aba ya neman taimakon kowa, har so uku ba za a rubuta masa laifin da ya aikata ba).

************************Musuc********************************

Masu Saurare, barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa, shirin na zababun aiyuka na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran,Hakika wannan dabi'a na daga cikin kyawawen dabi'un shugaban Annabawa Sahibin dabi'u masu girma da shaidar Alkur'ani mai girma kuma sahibin Isma Mutlaqa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka,a cikin Littafin Raudatul-Muttakin, an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce:(Ya Kasance Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ba ya tashi daga wani Majalisi (watau Wurin zama) koda kuwa bai jima a wurin ba sai ya nemi gafarar Allah madaukakin sarki watau Istigfari so 25).a cikin wani Hadisi na daban kuma an ruwaito Hadisi daga Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce:(Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya kasance yana Istigfari ko wani yini ko Rana so saba'in, Rawin sai ya tambayi Imam Sadik(a.s) kan yanayin Istigfari na Manzon Rahama ya shi Shin Haka Ma'aikin Allah yake cewa: أستغفر الله وأوب اليهsai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya kasance ya fadar cewa     أستغفر الله أستغفر الله so 70 أتوب الى الله أتوب الى الله so 70). Masu saurare ba boyayyan babu gare ku cewa Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya nisanta daga duk wani zunubi ko aibi.yawaita yin Istigfari neman gafara da kuma tuba zuwa ga Allah da yake yi shike nuna girman albarka da kuma hasken kyakkyawar dabi'ar sa, a cikin Littafin Hidayatul-Umma, an ruwaito Hadisi daga Shugaban Mumunai, kuma Shugaban wadanda suka dabi'antu da Dabi'um Muhammadiya, ya ce: Ma'aikin Allah (s.a.w.a) y ace (ku zamanto masu yawan neman gafarar Allah ta yadda iskar zunubai ma Ba za ta kusance ku ba), Allah madaukakin sarki ya sanya mu masu yawanta yin Istigfari ya kuma tsarkake mu daga duk wata dauda don albarkar riko da wasiyoyin Annabin Rahama Muhamadu Dan Abdullah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka.

**********************Musuc***************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu

 

 

 

Ra'ayi