Mar 05, 2016 09:47 UTC

Yau Alhamis 20 –Esfan-1394 H.Sh=30-Jamada-Ula-1437H.K.=10-Maris-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 140 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10-Maris-1876M. Alexander Garham Bell wani masanin ilmin kimiyar lissafi ya kirkiro wayar tarho a karon farko a duniya. An haifi Graham Bell a yankun Schotland na kasar Britania. Ya kuma fara da karantar da bebeyene, sanan ya kai ga tunanin kirkiro wayar tarko don tallafawa bebeyen. A nan bayan bincike da gwaje gwaje masu yawa ya sami nasarar kirkiro wayar tarho wacce ta sauya rayuwar mutane a duk fadin duniya. Banda haka Elexander Graham Bell ya kirkiro wani rubutu na bebeye don fahintar da su abinda mutane suke fada a rubuce.
02- Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 71 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10-Maris-1945M.  jiragen yakin kasar Amurka sun yi ruwan boma bomai a kan birnin Tokyo Babban birnin kasar Japan a lokacin yakin duniya na biyu. Jiragen yakin na Amurka sun yi ruwan boma bomain ne kan yankunan da fararen hula suke zama a birnin inda dubban mutane suka rasa rayukansu. Manufar wadan nan hare hare dai it ace tilastawa kasarn Japan Mika kai ga sojojin kawance a yankin duniya na biyu. Amma kasa Japan ta ki yin hakan har zuwa watan Augusta na wancan shekarar bayan boma boman nuklia wadanda jiragen saman yakin kasar ta Amurka suka jefa a kan biranen Hiroshima da Nagasaki na kasar ta Japan.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 31 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10-Maris-1985M. Konstantin Chernenko tsohon shugaban kasar tarayyar Soviet ya rasu. An haife shi a ranar 24-Satumba-1911M. a wani kauye a yankin saiberia na kasar Rasha. Bayan kamala karau yana dan shekara 18 a duniya Costintine ya kafa kungiyar matasan jam’iyyar gurguzu na kasar trayyar Soviet. Sai kuma shekaru biyu bayan haka ya zama babban sakataren jam’iyyar gurguzu. Daga nan ya ci gaba da samun girma a jam’iyyar har ya zama shugaban kasa . bayan watannin 10 da karban ragamar shugaban kasar tarayyar ne ya rasu a ranar 10-Satumba -1985M yana dan shekara 74 a duniya.

Tags

Ra'ayi